Safarar sassan jiki: Kotun Birtaniya ta samu Ekweremadu da aikata laifin da ake tuhumarsu.

Daga WAKILINMU

Kotun Birtaniya ta samu tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Ike Ekweremadu da matarsa, Beatrice, da aikata laifin safarar sassan jikin mutum.

Haka nan, laifin ya shafi har da wata ‘yarsu mai suna Sonia da kuma wani likita, Dr. Obinna Obeta, saboda taimakawa da suka yi wajen shirya kai matashin da lamarin ya shafa Birtaniya.

An same su da laifin haɗin baki wajen ɗaukar matashin zuwa London don cire ƙodarsa.

An rawaito cewar nan ba da daɗewa ba kotun da ke sauraren ƙarar za ta yanke hukunci kan shari’ar.

Idan za a iya tunawa, a watan Yunin 2022 ‘yan sanda a London suka cafke Ike Ekweremadu da matarsa bisa zargin safarar sassan jikin matashin da suka ɗauka zuwa ƙasar.

Bayanai sun ce sun nemi cire ƙodar matashin ne don dasa wa ‘yarsu.