Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya taya al’ummar musulmin jihar da na duniya baki ɗaya, murnar fara azumin watan Ramadan.
A sanarwar manema labarai mai ɗauke da sa-hannun mai magana da yawun Gwamnan, Alhaji Mamman Mohammed, ya ce Buni ya yi wa al’ummar musulmi kyakkyawan fatan samun dacewa a wannan wata mai alfarma wanda babbar dama ce ga musulmi saboda ɗimbin albarkar da watan ya ƙunsa.
“Ina taya mu murna baki ɗaya sakamakon ɗimbin alfanu da rahamar Allah Maɗaukakin Sarki dake cikin wannan wata mai girma, ina roƙon Allah ya ba mu lafiya da himma don mu girbi alfanun da watan ya ƙunsa.
“Kuma ya kamata mu zurfafa tunani, mu nemi gafarar Allah, mu zagaye kawunanmu da koyarwar Ramadan, mu inganta dangantakarmu, mu ci gaba da addu’o’in samun dauwamammen tsaro a jiharmu da kasarmu baki ɗaya.” In ji Gwamna Buni.
Har wala yau, ya jaddada burin gwamnatinsa wajen ci gaba da lalubo hanyoyin zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummar jihar.
“Za mu ci gaba da mayar da alkiblar mu kan gudanar da ayyukan da za su taimaki al’ummar tare da bunƙasa jindaɗi da walwalarsu.”
Buni ya buƙaci jama’ar jihar su ci gaba da bai wa gwamnatinsa cikakken haɗin kai da goyon baya a dukan aikace-aikacen ta na ci gaba a faɗin jihar.
Haka kuma, ya tunatar da al’ummar musulmi su dukufa wajen ayyukan ibada tare da addu’o’i, sabanin wufintar da lokutan zuwa ga abubuwa maras fa’ida ko jayayya da musu a wannan lokaci mai dimbin daraja.
Haka zalika, ya yi addu’a ta musamman ayi azumin watan Ramadan cikin nasara tare da gudanar da bukukuwan sallah a ƙarshen wannan wata na azumi.
Ya ce wannan ibada ta wata ɗaya mai muhimmin tanadi a addinin musulunci, wanda ya fara yau (Alhamis) sakamakon ganin jinjirin wata a wurare daban-daban a wannan jihar da sauran sassan duniya.