Hukumar wasannin guje-guje ta haramta wa mata-maza shiga gasar wasannin mata

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta tabbatar da cewa za ta fitar da ’yan wasa mata-maza waɗanda suka sauya halittarsu daga maza zuwa mata daga shiga gasar mata.

Shugaban hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya, Lord Coe ya ce, “Mun kuma ɗauki kwakkwaran mataki don kare nau’in mata a wasanninmu, da yin hakan ta hanyar taƙaita shigar ’yan wasa mata-maza.

“An hanke shawarar ne tare da tuntuvar masu ruwa da tsaki da dama da suka haɗa da ƙungiyoyin mambobi 40, da ’yan wasanmu, da masu horar da mu da kuma ta hukumar ’yan wasa, da kuma sauran ƙungiyoyin al’umma da suka haɗa da ƙungiyoyi masu zaman kansu, ƙwararrun Majalisar Ɗinkin Duniya.

“Yawancin wazanda aka tuntuɓa sun bayyana cewa bai kamata ‘yan wasan mata-maza su kasance cikin fafatawa a ɓangaren mata ba,” in ji shi.