Daga BASHIR ISAH
Majalisar Dokokin Jihar Ondo ƙarƙashin jagorancin Kakinta, Olamide Oladiji, ta ayyana Mataimakin Gwamnan Jihar, Lucky Aiyedatiwa a matsayin muƙaddashin gwamna.
Hakan ya biyo bayan wasiƙar da majalisar ta ce ta samu ne daga Gwamnan Jihar, Oluwarotimi Akeredolu, kan buƙatar miƙa ragamar mulkin jihar ga mataimakimsa kasancewar zai tafi hutun jinya.
A ranar Laraba, Kakakin majalisar ya ayyana Aiyedatiwa a matsayin muƙaddashin gwamnan jihar a Akure, babban birnin jihar.
A cikin sanarwar da ya yi a zauren majalisar, Kakakin ya ce: “Biyo bayan shawarar da likita ya bayar ta buƙatar zuwa duba lafiyarsa, Gwamnan Jihar Ondo, Oluwarotimi Odunayo Akeredolu, ya gabatar wa Majalisar wasiƙar ɗaukar hutun tafiya jinya.
“Matakin da Gwamnan ya ɗauka ya yi daidai da Sashe na 190 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya.
“Don haka yanzu mataimakinsa, Hon. Lucky Aiyedatiwa, zai ci gaba da riƙe ragamar mulki a madadin Gwamnan a matsayin muƙaddashi har zuwa loakcin da Gwamna zai dawo.
“Ana sa ran hutun da Gwamna ya ɗauka ya fara aiki daga ranar Laraba, 13 ga Disamba, 2023,” in ji Kakakin Majalisar.
