Rashin ofis da abin hawa a Kano ne ƙalubalenmu a shekara 50 da kafuwa – JNI

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Shugaban Jama’atu Nasril Islam (JNI) na ƙasa, reshen Jihar Kano, Malam Muhammad Nuraddeen Gwagwarwa, ya bayyana cewa shekaru 50 kenan da kafuwar ƙungiyar, sai dai babbar matsalar da take fuskanta a Kano ita ce rashin ofis da abin hawa. Ya ce duk da cewa gwamnatocin da suka gabata sun taimaka sosai wajen inganta addini, amma JNI a Kano ta daɗe tana neman tallafin da bai samu ba.

A yayin taron tunawa da cikar ƙungiyar shekaru 50, Malam Gwagwarwa ya ce an kafa JNI ne domin bayar da agajin gaggawa ga masu buƙata—musamman masu fama da hatsari, rashin lafiya, ko wani mummunan lamari—tare da yaɗa ilimi, wayar da kai, da aikin da’awa. Ya ce duk da rawar gani da ƙungiyar ke takawa wajen ceto rayuka, har yanzu babu ofis, babu motar aiki a Kano.

Shugaban JNI ya tunasar da irin gagarumin tasirin ƙungiyar lokacin tashin abubuwan fashewa a Kano, inda ‘ya’yan ƙungiyar suka mamaye tituna da asibitoci suna taimakon al’umma, lamarin da har ya sa tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso jinjinawa ƙoƙarinsu. Ya roƙi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya tallafa wa ƙungiyar, musamman bayan rasuwar babban mai daukar nauyin ta, marigayi Alhaji Aminu ɗantata.

Ita ma da take jawabi, Sakatariyar JNI ta Kano, Hajiya Amina Haruna Shanono, ta ce ƙungiyar na da mata mambobi dubban-dubban a faɗin ƙasa masu aikin agaji da shiga lungu da saƙo domin ceton rayuka. Ta yi kira ga hukumomi da masu hannu da shuni da su tallafa wa JNI domin aikinta na ƙasa da ƙasa.

By ukarofi