Tsadar taki za ta iya kawo ƙarancin abinci a Nijeriya – AFAN

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Shugaban All Farmers Association of Nigeria (AFAN), Malam Rabiu Faruk Mudi, ya yi gargaɗin cewa tsadar taki, magungunan ƙwari, da sauran kayan aikin gona na iya janyo raguwar noma a Nijeriya idan ba a ɗauki mataki ba. Ya bayyana haka ne yayin taron wayar da kan manoma a bikin Ranar Abinci ta Duniya a Kano.

Malam Mudi ya ce hauhawar farashin kayayyakin aikin gona ya sanya manoma da dama kasa iya ci gaba da noma, duk da cewa a yanzu kayan abinci a kasuwa sun samu sauƙi. Ya buƙaci Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sa baki wajen sauƙaƙa farashin kayan aikin gona, domin kaucewa matsalar ƙarancin abinci nan gaba.

A nasa ɓangaren, Farfesa Abba Gambo, mai ba wa gwamnonin jihohi shawara kan harkokin noma, ya ce an cimma ci gaba a taron ta hanyar gabatar da ingantattun iri daga cibiyoyin bincike—kamar gero da shinkafa—domin inganta gina jikin al’umma. Ya yi kira ga gwamnonin Nijeriya da su yi amfani da shawarwarin masana wajen samar da kayan aikin gona cikin sauƙi.

Shugaban cibiyar binciken harkokin noma ta Jami’ar Bayero Kano (CDA), Farfesa Sunusi Gaya, tare da mataimakinsa Dr. Murtala Muhammad, sun bayyana cewa jami’ar ta samar da ingantattun iri da zasu tallafa wa ci gaban noma a Nijeriya da Afirka baki ɗaya.

By ukarofi