Gwamnan Jigawa ya ɗauki matakin kawo ƙarshen mutuwar mata a lokacin haihuwa – Turakin Taura

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi (ɗanmoɗi), ya ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalar yawaitar mutuwar mata a lokacin haihuwa a ƙaramar Hukumar Taura. Wannan na zuwa ne bayan rahotannin masana lafiya da suka nuna yankin na daga cikin mafi fama da matsalar.

Shugaban ƙaramar Hukumar Taura, Hon. Shuaibu Ibn Hambali Zarga (Turakin Taura), ya shaida wa manema labarai cewa Gwamnan ya bada umarni a gyara asibitoci baki ɗaya, lamarin da ya sa aka inganta babban asibitin Taura da ya dade cikin yanayi mara kyau fiye da shekaru 30. Gwamnan zai kaddamar da asibitin da kansa nan ba da jimawa ba.

Turakin Taura ya tabbatar da cewa sauran asibitoci ma suna samun gyare-gyare, tare da shirye-shiryen ba wa dubban jama’a tallafin kula da lafiya kyauta. Ya ce gwamnati ta kuma tallafa wa matasa 8,000 da kayan sana’o’i, ta buga littattafai fiye da 88,000 domin rarrabawa ɗalibai, tare da gudanar da gyaran makarantu da samar da sababbin ajujuwa.

Ya ƙara da cewa an buga takardun kammala firamare 15,000 domin kawar da matsalar da ɗalibai ke fuskanta a baya. Haka kuma an ɗauki malaman tallafi 125 domin inganta harkar ilimi. A karshe ya yaba wa Gwamna Namadi bisa siyan jami’ar Khadija da gina manyan hanyoyi uku a cikin ƙaramar Hukumar Taura, tare da yabawa haɗin kai da al’umma da ma’aikata ke bayarwa.

By ukarofi