Rashin tsaro zai zama tarihi a Katsina – Gwamna Raɗɗa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya sha alwashin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ya addabi wasu sassan jihar a wannan shekarar da aka shiga.

A saƙon shi na murnar shiga sabuwar shekara Malam Dikko Raɗɗa ya ce duk da matsalar tsaro ta zama ƙalubale a ƙasar baki ɗaya,a nan Jihar Katsina gwamnati ta ɗauki matakai da dama na kawo ƙarshen matsalar a jihar.

Kan haka ne gwamnan ya ce gwamnatin sa a karo na biyu ta ɗauki jami’an tsaro na al’umma (CWC) tare da samar masu da abun hawa da sauran kayan aiki.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati ta samar da kayayyakin zamani na jami’an tsaro a jihar da zai taimaka masu wajen yaƙi da ta’adanci.

Ya kuma sanar da cewa gwamnatin sa ta sami cigaba wajen fannin ilimi da harkan noma da kiwon lafiya a shekarar da ta gabata.

“Yanzu haka gwamnati ta tura ɗalibai 68 da zasu yi karatu kan fasahar zamani”gwamnan yace.

Wajen fanin noma,gwamnan ya bayyana cewa manoma 30,000 suka amfana da tallafi na kuɗi, takin zamani da sauran kayan noma domin taimaka masu wajen noman rani.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙara da bayyana cigaba da aka samu kan kiwon lafiya da gina hanyoyi da tallafawa masu ƙanana da matsakaici sana’o’i.

Yace a wannan shekara gwamnati za ta maida hankali wajen tabbatar da tsaro da inganta aikin gwamnati.

Malam Dikko Raɗɗa ya yabawa alummar jihar kan haɗin kai da suke bai wa jami’an tsaro musamman wajen bada bayanai na sirri wanda hakan ya taimaka wajen rage ta’adanci a jihar.

“Ina mai bada tabbacin a wannan shekara tsaro zai inganta, gwamnati za ta samu aiwatar da aikace-aikace na bunƙasa ƙasa, manoma zasu koma gonakin su, walwalar jama’a zai ƙaru”Dikko ya ce

By ukarofi