Rashin tsayayyen farashin Dala na dagula harkar kasuwanci – Yusuf Maiwake

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana ta’azzarar  farashin Dala da cewa yana dagula harkar kasuwancin ‘yan kasuwar hatsi na Dawanau da ya sa suka ma rasa yaya za su yi. Alhaji Yusuf Barau Maiwake jigo a kayan amfanin gona na Dawanau shi ya bayyana haka.

Ya ƙara da cewa, Dala ta zama abinda za ka ji yanzu an ɗaga farashinta, an jima  za ka ji farashin ya sake hawa, tun da su kayansu waje ake fitarwa kuma da Dalar ake amfani. Idan farashin bai tsaya ba, kowane ɗan kasuwa yana cikin ruɗani.

Ya ce da a lokaci irin wannan, idan kaka ta fara kayan abinci araha yake. Amma bana yadda kayan abinci suka yi tsada, ba su taɓa ganin irin haka ba.

Alhaji Yusuf Barau Maiwake ya ce, sama da shekaru 30 yana cikin wannan harkar ta sayar da kayan abinci. Amma ba su taɓa ganin shekara irin wannan ba. Suna so Gwamnati ta tsaya ta tabbatar da farashin Dala ya dawo dai-dai yadda ya kamata. Domin idan aka cigaba da irin wannan tafiyar, Allah ne ya san me zai faru. Mutane da yawa za su shiga cikin matsala.

Da ya juya Kan ƙoƙari da ake na haɓaka Kasuwanci a kasuwar Dawanau ta hanyar zamani bisa yunƙurin da Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero yake, cewa ya yi yun}urin ba ƙaramin hoɓɓasa ba ne.

Alhaji ya ce, kasuwar  yanzu mai jari shi yake kasuwanci. Baƙi ‘yan waje su suke zuwa da kuɗi kasuwar Dawanau. Kusan a iya ganin ta zama tamkar kasuwarsu  tasu ta kansu.  Su suke yin farashi da yanda za a yi.

Alhaji Yusuf ya bayyana cewa, da irin wannan kasuwar da ake nuna musu  ta zamani, za su san abinda ake ciki a kasuwa. Tsarin da za a  kawo ba ƙaramin cigaba ne ga ‘yan kasuwar ba.