Raya ya zama gwarzon ɗan wasan Arsenal na Satumba

Spread the love

David Raya ne ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan wasan Arsenal na watan Satumba, wanda magoya bayan ƙungiyar suka zaɓa.

Wanda ya lashe safar zinare a matakin wanda ƙwallaye da yawa bai shiga ragarsa ba da a bara, karon farko da ya zama gwarzon Gunners na wata.

A labarin da Arsenal ta wallafa a shafinta na Intanet, Raya ya doke wadanda suka yi takara da ya haɗa da Gabriel da Bukayo Saka da William Saliba ka ƙuri’a kaso 44 cikin 100.

Ya buga wasan Tottenham ƙwallo bai shiga ragarsa ba da taka rawar gani a Atlanta da tare penaritin Mateo Retegui, inda Gunners ta samu maki a Italiya.

Haka kuma ya taka rawar gani a wasan da Arsenal ta je ta tashi 2-2 a Etihad da Manchester City da doke Leicester City 4-2 a gasar firimiya.

Raya shi ne mai tsaron raga na farko da ya lashe ƙyautar gwarzon Arsenal na wata-wata tun bayan Aaron Ramsdale a Nuwambar 2021.

By ukarofi