
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Lahadi tsohon Shugaban Ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya yi jimamin rasuwar tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Alhaji Bamanga Tukur, wanda ya rasu kwanaki kaɗan ya cika shekaru 91 a duniya.
Obasanjo a wata sanarwa da ya fitar a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, ya bayyana marigayin a matsayin “mai kishin ƙasa”, wanda rayuwarsa ta kasance shaida ga kishi, ƙoƙari mara iyaka kuma jajirtacce wajen hidimta wa al’umma.
A sanarwar, wadda kakakinsa, Kehinde Akinyemi ya aike wa manema labarai, Obasanjo ya ce, marigayin ya bayar da gagarumar gudunmawa a fannonin shugabanci, harkokin ƙasa-da-ƙasa, jagorancin siyasa bisa ƙwarewa da sadaukarwa.
Ya tunatar da rawar da Bamanga Tukur ya taka a lokacin da yake riƙe da muƙamin shugaban Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Ƙasa (NPA) da matsayinsa na Gwamnan tsohuwar Jihar Gongola da kuma Ministan Masana’antu, wuraren da ya ce ya taimaka wa nasarorin ci-gaba da suka shafi al’umma da ma ƙasa baki ɗaya.
Tsohon shugaban ƙasar ya ƙara da cewa, marigayin ya kuma samar da salo da tsare-tsaren tafiyar da lamuran dimukraɗiyya bisa tsari a lokacin da ya riƙe muƙamin shugabancin PDP a matakin ƙasa daga 2012 zuwa 2014. A cewarsa, rasuwarsa babban rashi ne ga Nijeriya, wanda ya samar da giɓin da zai yi wahalar cikewa a tarihin Nijeriya.
A ƙarshe, a madadin iyalansa Obasanjo ya miƙa saƙonsa na ta’aziyya ga iyalai, gwamnati da al’ummar Adamawa da ma abokan harkar siyasa bisa rashin, yana mai addu’ar Allah ya jiƙansa ya kuma gafarta masa kurakuransa, sannan ya sanya shi a gidan aljanna tare da bai wa makusanta haƙurin juriyan rashin sa.
