Rayuwata na cikin hatsari bayan janye mini jami’an tsaro – Sanata Lado

Daga UMAR GARBA a Katsina

Ƙasa da sa’o’i 24 kafin gudanar da zaɓukan gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi ɗan takarar Gwamnan Jihar Katsina a Jam’iyyar PDP, Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke, ya zargi Babban Sufeton ‘Yan Sanda da janye masa jami’an dake tsaron lafiyarsa.

Sanata Lado ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da gidan Talabijin na Channels a cikin shirin ‘Sunrise Daily’ wanda Manhaja ta bibiya.

A cewarsa, an janye masa jami’an tsaron ne tun mako biyun da suka gabata saboda bambancin ra’ayin siyasa.

“Muna fuskantar tsangwama da barazana daga gwamnati, rayuwata na cikin hatsari maganar da nake yi yanzu haka, AIG ya janye mini jami’an tsaro, kuma babu wani dalili da aka ba ni dangane da hakan”. Inji shi.

Sanata Lado ya ce ya kira taron manema labarai don sanar da duniya irin hatsarin da yake fuskanta dangane da janyen masa jami’an tsaron amma duk da haka babu wata amsa da ya samu daga wajen mahukunta.

Ɗan takarar gwamnan ya ce janye jami’an tsaron bai sanyaya masa gwiwa ba, hasali ma ya ƙara masa ƙarfin gwiwar lashe zaɓen gwamnan jihar wanda za a gudanar ranar Asabar.

“Na shirya lashe zaɓen gwamnan da za a gudanar, kuma ni ne zan yi nasara duba da yadda al’umar jihar a ƙananan hukumomi 34 suka karɓe ni,” in ji shi.