Wadata a Musulunci

Manhaja logo

Daga MUHAMMAD M. MUSTAPHA

Talauci ɗan uwan kafirci, in ji malaman zaure. Al-Imamul Gazali a littafinsa Ihya’u Ulumiddin yana cewa: ‘rabauta a lahira ba za ta samu ba sai addinin mutum ya gyaru, addini ba zai taɓa gyaruwa ba sai duniyar mutum ta tsaru, duniya ba za ta taɓa tsaruwa ba sai sana’u da harkokin naiman arziƙi sun tsaru’, tsaruwar sana’u da harkoki kuma su ke korar talauci da samar da wadata da nutsuwa, wani abu da malaman zamani ke kira da gyaruwar ɗan Adam a farko kafin gudanar ibadun addini”, ko al-insaniyyatu qablat tadayyin. Malam Sufyan Assauri ya na cewa: ‘a da kuɗi abin ƙyama ne, amma a yanzu garkuwar mumini ne’.

Wata rana ya baiwa wani ɗalibinsa jari, kuma ya umarce shi da ya kula da jarin nan sosai, sannan yace da shi: ‘kai ba da ban kuɗin nan ba da waɗannan masu mulkin (da masu abin duniya) sun yi yadda suka gadama da mu’.

An rawaito cewa Luƙamnul Hakim yana faɗa ga ɗansa cewa: ‘babu mutumin da talauci zai cimma face ya yi masa ɓarna a addininsa, hankalinsa da mutuncinsa haɗi da samar masa da ƙasƙanci a cikin mutane’. Abu Zaid, Jarumin ƙirƙirarrun labaran littafin Muƙama cewa yake banda tsoran Allah da ya yi wa dukiya da wadata, saboda amfaninsu a duniya da lahira, kirarin Ƙudra maɗaukakiya!

Hanyoyi da yawa Musulunci ya bayyana don samun ficewa daga ƙuncin babu da gamdakatar da arziƙi da wadata, hanyoyi na sunnar rayuwa waɗanda za su yi aiki ga kowa-da-kowa kuma a ko-ina-da-ina. Daga cikinsu, a farko, dagewar Mutum da yaƙarsa munanan ɗabi’u takwas masu gaba da arziki da wadata.

Gajiyawa ko kasa gudanar da abinda ya kamata a gudanar, kasala, zama cikin damuwa da rashin nishaɗi, dawwama a cikin fushi ɓacin rai da baƙin ciki, tsoro na rashin kutsawa cikin al’amurran naima da fafutuka, rowa ta lokaci, tunani da abin hannun ga barin sanya su cikin abinda aka saka a gaba mai amfani, ɗaukar nauyi na abinda yafi ƙarfin mutum dangane da lokacinsa da abinda yake samu, na takwas kuma sako-sako da baiwa abokan hulɗa kafofi da damar danne mutum a cikin harkoki.

Wannan ita ce ƙoyayyiyar manufa abar fahimtowa daga addu’ar da Annabi (SAW) ya baiwa Abu Sa’id Alkhudri (RA); Allahumma inni a’uzu bika minal hammi wal huzni, wa a’uzu bika minal ajzi wal kasli, wa a’uzu bika minal jubni wal bukhli, wa a’uzu bika min galabatid daini wa ƙahrirrijal.

Faɗaɗa sanayyar mutane da naiman ƙarin sababbin abokan hulɗa, ɗaya ce cikin hanyoyin da Musulunci ya nusar na dabarun naiman arziƙi da wadata. Annabi (SAW) yana cewa: ‘duk mai son a yalwanta masa arziƙinsa, kuma a jinkirta masa a gurbinsa; to ya sadar da zumuncinsa’. Kowane mutum a duniya ɗan Adamu ne; kowane mutum a duniya abokin sada zumunci ne!

Kazar-kazar, motsi da shige da fice a wurare da garuruwa dabara ce cikin dabarun da Musulunci ya nusar wajen naiman arziƙi da wadata. Al-Ƙur’ani Mai Girma ya ba mu labarin cewa halin matsin rayuwa da rashin abin hannu da Sahabbai suka shiga a wani lokaci a zamanin Annabi (SAW) ya faru ne sakamakon zagaye su da abokan gaba su ka yi da rashin samun damar tafiye-tafiye, domin tafiya mabuɗi ce na arziki. Abdullahi ɗan Umar yana cewa: duk ɗan kasuwar da ya samu matsin arziki a wani gari to ya maida kasuwancinsa zuwa wani garin daban.

Dabarbarun naima ke nan, hanyoyin vuvvugowar arzikin fa? Al-Ƙur’ani Mai Girma, a wurare da dama ya yi maganar ayyuka, sana’u da hanyoyin samu don gudanar rayuwar duniya; abinda Al-Imamul Gazali ya harhaɗa ya kasa gida uku. Kaso na farko, abinda ya kira da zuciyar sana’u. Idan babu su babu rayuwa. Waɗannan sune: noma da kiwo, saƙa, gini, sai kuma shugabanci da siyasa.

Siyasa tana nufin gyaran rayuwar mutane, gyaran jikkunansu (likitanci), gyaran halayensu da mu’amalarsu da gyaran muhallinsu da abubuwan dake kewaye da su. Ƙere-ƙere (ko technology a zamanance) su ne kaso na biyu. Na uku kuma sana’un ado da ƙawata rayuwa da sana’un da ke taƙama da abubuwan da aka ambata a kaso na farko kamar girki da sauransu.

Ta wata fuskar kuma, Malaman addinin Musulunci sun bayyana hanyoyin korar talauci na cuɗanni-in-cuɗeka – hanyoyin da Musulunci ya tsara su a kan sauƙaƙa rayuwa, cin halak, kiyaye dukiya, ’yanci da samuwar amfani ta kowace fuska don samun arziki.

Hanyar musaya, ban gishiri na baka manda ko cinikayya ita ce ta farko. Aikatau da bayar da haya na biye a baya. Tarewa (company), da ƙirala, ma’ana karvar wakilcin gudanar da dukiya daga mai ita, duka hanyoyi ne na samun wadata.

Sai dai tare da waɗannan dabarbaru da hanyoyi, babu wani abu da zai samu ko ya gudana sai abinda Allah ya so. Allah ne mai yalwanta arziki ga wanda ya so, shi ke ƙuntatawa ga wanda ya so. Mai ne ne abin yi yayin da duk dabaru da hanyoyin da aka ambata a baya suka kasa damuwa a tare da mutum?

Amsa na nan cikin tarihin Annabawa guda biyu: Annabi Musa da Annabi Sulaimanu (AS).

Akwai kamanceceniya mai yawa tsakanin tarihin Annabi Musa da na Annabi Sulaimanu wanda Al-Ƙur’ani ya bayar – ya bayar saboda hikma don a lura.

Kowannansu Allah ya bamu labarin hanyar da ya samu matar da ya aura.

A saboda tsuntsun Alhududu ya fanshi kansa daga azabar da ke fuskantarsa a dalilin tafiya da yayi ba izni daga fadar Annabi Sulaimanu, ya bada labarin Sarauniya Bilkisu.

Daga nan ya ɗauki saƙon Annabi Sulaimanu zuwa gare ta, abinda ya jawo tahowarta daga garinta, daga fadarta, zuwa fadar Annabi Sulaimanu. Wannan shi ya kawo aurenta da Annnabin Allah. Ta vangaren Annabi Musa kuwa, shi da kansa ne ya guje wa fadar Fir’auna, abinda ya qaddara masa zuwa madyana har ya haɗu da matar da ya aura.

Jama’ar Annabi Sulaimanu su ke da mulki da iko da wadata da damar yin uƙuba da azabtarwa. Mutanen Annabi Musa kuwa su ake da ikon azabtarwa tsanantawa da ƙuntata wa rayuwarsu ko ta ina.

Abin la’akari a nan, duk lokacin da mutum ya samu kansa a yanayin wadata da iko to zai yi abinda Allah SWT ya umarci gidan su Annabi Sulaimanu su aikata; mutum ya yi aikin godiya ga Allah, shi ne aikin raya ƙasa da ’yan ƙasa (maqamus Shukr). I’imalu ala Dawuda shukra . Idan kuwa ya samu kansa a takura, rashi da matsin rayuwa, to aikinsa bin umarnin abinda Annabi Musa ya faxɗa ga jama’arsa, ista’inu billahi wasbiru, ku jure ku naimi taimakon Allah (maƙamus Sabr).

Nassoshin Al-Ƙur’ani da Sunna sun nuna mana hanyoyin naiman taimakon Allah a wajen naiman arziki da wadata. Lazamtar Taƙwa, Addu’a, Sadaka, Sallah, Istigfari da Tasbihi duk hanyoyi ne wanda malamai suka yi dogon sharhi a kai a wannan mas’ala.

Allahumma inna na’uzu bika minal kufri wal faƙr.