
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Zakaran ɗan wasan Real Madrid ta ƙasar Sifaniya, Vinicius Jr na shirin cigaba da tattaunawa kan batun kwantaragi da ƙungiyar a wannan makon, yayin da wadda ta lashe Premier League a kakar wasan da ya gabata, Arsenal ke cigaba da nuna kwaɗayinta kan ɗan wasan gaban.
Arsenal ta zaɓi ɗan Brazil ɗin a matsayin wanda take fatan saye don ƙara wa gefen hagunta ƙarfi matuƙar Madrid ta gaza daidaitawa da shi.
Saidai duk da raɗe-raɗin komawar Vini Arsenal ya ɗauki hankalin magoya baya, har yanzu akwai rashin tabbas na yiwuwar komawarsa a wannan bazarar.
Real da wakilan Vinicius na tattaunawa kan sabon kwantaragin tun tsawon watanni 18. Kwantaraginsa na yanzu zai ƙare ne a 2027.
A kwanan nan ne ɗan wasan ya koma cikin tawagar Madrid bayan kammala hutunsa na ƙarshen kakar da ta gabata da kuma gasar Kofin Duniya na 2026.
Sabon kociyan ƙungiyar, Jose Mourinho na son damawa da shi cikin ‘yan wasansa, yana mai fatan ya rattaɓa hannu a sabon kwantaragi.
Haka shi ma Vini yana fatan cigaba da zama a Bernabeu amma kwantaraginsa zai kare a bazara ta gaba, yayin da Real ke fargabar rasa shi a matsayin kyauta ga wata ƙungiya.
