Rigakafin korona: Lai ya musanta cewa Nijeriya na yawo da ƙoƙon barar neman tallafi

Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ƙaryata ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa kan cewa Nijeriya na kewayawa sassa tana miƙa ƙoƙon baranta na neman a tallafa mata da allurar rigakafin koroa.

Ministan ya yi wannan ƙarin hasken ne yayin wata tattauna da kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ran Laraba, a Abuja.

Ministan ya ce wasu daga cikin rigakafin Nijeriya ta sayo su ne ta hannun Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Afrika (AU) wadda aka cimma yarjejeniyar samar da rigakafin korona guda milyan 400 ta hanyar ciwo bashi a bankin AFREXIMBANK don amfanin ƙasashe mambobin AU.

Don Haka Mohammed ya ce, “Ba daidai ba ne a ce mun dogara ne da tallafi, don kuwa rigakafi ba kamar burodi ba ne da za ka tafi shago ka sayo.”

Ya cigaba da cewa saboda irin tsarin da ke tattare da raba maganin rigakafi, hatta su masu yin maganin ba su son sayarwa, “Wannan ne ya sa dole muka bi ta hannun AU don ta samo rigakafi guda milyan 400 don amfanin Afirka baki ɗaya.

Ba wai kawai muna sa ran samun rigakafin mai yawa ba wanda gwamnati ta saya da kuɗinta, muna ma ƙoƙarin ganin yadda za mu ƙirƙiro namu rigakafin na cikin gida “

Daga nan, Ministan ya taɓo batun yadda Majalisar Zartarwa a watan Yuni ta amince da a kashe Naira biliyan N83.56 wajen sayo rigakafin korona guda milyan 30.

Lamarin da Ministan ya bayyana da cewa an samu haɗin kai tsakanin Gwamnatin Tarayya da cibiyoyin bincike daban-daban dangane da yadda za a yi Nijeriya ta ƙirƙiro nata rigakafin ta yadda ba sai ta ƙetara zuwa ƙasashen waje ba.