Rikicin ƙabilanci ya ci mutum biyar a kan iyakar Gombe da Adamawa

Daga AISHA ASAS

Kimanin mutum biyar ne aka ruwaito sun rasa rayukansu sakamakon rikicin ƙabilanci da ya auku a yankin garuruwan Nyuwar/Jessu masu maƙwabtaka da juna a kan iyakar Gombe da Adamawa inda ƙabilun Waja da Lunguda ke da zama.

Wani ganau da ya shida faruwar rikicin ya bayyana cewa saɓanin ya faru ne sakamakon rashin jituwar da aka samu tsakanin maharba daga Jessu da kuma Fulanin Lunguda a Adamawa, waɗanda tun ba yau ba babu alaƙa ta lumana a tskaninsu.

Majiyar Manhaja ta ce yayin da maharban Jessu suka tafi daji farauta ne sai matasan Fulani suka tsinkaye su nan take suka fasa kuwar kiran ‘yan’uwansu.

A cewar majiyar, “Abin da muka fahimta shi ne a lokacin da yaran Fulani suka ga maharban sai suka soma kuwar wai sun kawo musu hari tare da shaida wa mahaifinsu batun.

“Zuwan Fulanin ke da wuya sai suka kama harbi, har zuwa wannan lokaci da nake magana faɗan bai tsaya ba, suna ta kone-ƙonen gidaje.”

Ya zuwa haɗa wannan labari, da aka nemi jin ta bakin Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Ishola Babaita, ya ce ba shi da ta cewa har sai ya je wurin da rikicin ya auku ya gane ma idanunsa.

Haka nan Manhaja ta samu labarin shi ma Gwamna Inuwa Yahaya da wasu jiga-jigan gwamnatinsa na daga cikin waɗanda suka tafi don ganin yadda lamurra suka kasance a yankin.

Rikicin wanda ya auku a wannan Talatar, ya yi sanadiyyar Gwamnantin Gombe ta ɗauki matakin kafa dokar hana zirga-zirga na sa’o’i 24 a yankin ƙaramar hukumar Balanga wanda kuma ya soma aiki nan take.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Njodi, ya ce an tura jami’an tsaro zuwa yankunan da rikicin ya shafa domin kwantar da tarzomar da ta tashi.