Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Alƙalin babbar kotun jihar Gombe mai lamba ta bakwai, Mai Shari’a Fati Musa, ta janye daga ci gaba da sauraron ƙarar rikicin fili da kamfanin Emir General Integrated Limited ya shigar da Grand Scope Construction Company kan zargin bijirewa umarnin kotu.
Shari’ar ta rikicin fili ta shafe watanni tana gudana, inda kotun ta ba da umarnin dakatar da duk wani aiki a filin, amma kamfanin gine-ginen ya ci gaba da aiki duk da umarnin.
A zaman kotun na ranar Laraba, Mai Shari’a Fati Musa ta bayyana cewa ba za ta ci gaba da sauraron ƙarar ba saboda son zuciya ya shiga lamarin.
Ta ce za ta miƙa takardun ƙarar zuwa Babban Jojin jihar domin ba wani alƙali damar ci gaba da sauraron shari’ar.
A wata hira da aka yi da Lauyan kamfanin Grand Scope Construction Company, Barrister Daniel Tsaro, ya bayyana matakin alƙalin a matsayin wanda ya dace da ƙa’idar shari’a. Ya ce.
“Ba wannan ne karo na farko da wani alƙali ya janye daga shari’a ba saboda irin wannan yanayin.
Wannan mataki na iya taimakawa wajen tabbatar da adalci.”
Shi ma Suleiman Abdurrahim, lauyan kamfanin Emir General Integrated Limited, ya bayyana cewa matakin alƙalin ya dace da dokoki. Ya ce.
“Idan alƙali ya ce yana da dalilin kansa da ya hana shi ci gaba da sauraron shari’a, yana da cikakken iko kan wannan matakin.”
Ya kuma ƙara da cewa sun gabatar da buƙatar dakatar da ginin da ake yi a filin da ake rikici a kai, yana mai nuna ƙwarin gwiwa cewa sabon alƙali zai tabbatar da adalci yayin da shari’ar za ta ci gaba.
An gano cewa filin da ake rikici a kai yana kan hanyar Gombe zuwa Bajoga, kuma gwamnati ce ta bai wa kamfanin Grand Scope Construction kwangilar gina sansanin makamai a wurin, abin da ya sa rikicin ya ƙara ɗaukar hankali.
Yanzu dai ɓangarorin biyu na jiran naɗin sabon alƙali da zai ci gaba da sauraron ƙarar.
Wannan matakin na janye wa daga shari’ar ya ƙara jan hankalin al’umma kan batun da ke cike da cece-kuce.
