Tasirin kitso da lalle a kwalliya

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Masu bibiyar Manhaja sannunku da ƙoƙari, barkanmu da sake kasancewa da ku a shafin Kwalliya.

A yau zamu tattauna ne kan tasirin kitso da lalle a kwalliya. Saidai kafin nan, za mu fara da matsayin kitso da lalle a ƙasar Hausa.

Idan muka fara da lalle, za mu iya cewa, ba za mu kira shi a matsayin al’ada kawai ba, kamar yadda na ji wani hadisi, wanda ba zan iya faɗar sahihancinsa ba, ya yi bayyanin yadda lalle yake sunnah, kasancewar Manzon rahma (S.A.W) ya ba wa wani umurnin saka lalle a lokacin da ya yi aure.

Da wannan za mu iya cewa, matsayin lalle babba ne, don haka ba za mu iya kiransa da al’ada kawai ba.

Shi ma kitso bai kasance al’ada ta malam Bahaushe kawai ba domin mutane a sassa daban daban na duniya na kitso a matsayin ƙawa.

Saidai tunda muna magana ne kan Hausawa, za mu iya cewa ɗaya daga cikin al’adu da aka riƙa da matuƙar muhimmanci a ƙasar Hausa, lalle da kitso na a layin, inda wadda ke yawan yin su ake mata laƙabi da mai tsafta.

Za mu iya cewa, kitso zai iya shiga a layin tsafta, amma ga mai yin sa, domin akwai mutanen da ba ma’abuta kitso ba ne, amma suna gyara shi akai-akai.

Sai dai bari mu je ga muhimmancinsu a gidan aure.

Akwai wata rana da na ji an yi saki saboda rashin yin lalle, kuma ba a fi shekaru huɗu ba na sake jin wata mijinta ya sake ta saboda tana yin lalle.

Abin nufi a nan dai ba za mu iya cewa kitso da lalla na gyaran aure ba, dalilin kowanne namiji da irin ra’ayinsa. 

Za mu ci gaba a mako mai zuwa.

By ukarofi