Ƙarin aure a wurin malam bahaushe (2)

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya, Allah Ya sa mu dace da rahmar duniya da ta lahira.

A makon da ya gabata, mun fara kwararo bayani kan ƙarin aure, inda muka soma da bayanin halaccin yin mace fiye da ɗaya, zuwa inda muka soma bayani akan ababen da ya kamata a yi dubiya kafin a ƙara aure.

Mun kawo ƙarfin aljihu a matsayin ɗaya daga cikin ababen da ya kamata a yi dubiya kansu kafin ƙarin aure, kasancewar ci da sha da kuma muhalli yana wuyan miji.

Abu na biyu, wanda za mu soma kansa shi ne, lafiyar sauke haƙƙin aure. A nan ba wai ina magana kan iya lafiyar iya kusantar mace ba, har da halitta ta sha’awa.

Kamar yadda muka sani, a ɓangaren sha’awa ma Allah ya halicci mutane mabambanta, kamar yadda ya yi fari, baƙi, dogo da kuma guntu. Haka ma a ɓangaren sha’awa, akwai hariji, akwai mutawasiɗi, akwai kuma dakhili.

A ɓangangare na farko, shi ne namijin da mace ba ta isar sa, wanda a nasa ɓangaren ko mata nawa ne zai iya aura. Kuma ba a iya maza ne kawai ake samun wannan ɓangaren ba, har a mata, mun karkata ne da faɗin namiji domin darasin namu a nan ya karkata.

ɓanagare na biyu kuwa akwai matsakaici, shi dai ba hariji ba, kuma shi ba wanda ba shi da sha’awa ba. A wannan fagen an fi komai samun matsala, domin a irin waɗannan mutane za ka iya samun namijin da zai iya zama da mata huɗu kuma komai lafiya ba tare da ya tauye haƙƙin wata daga ciki ba. Haka kuma za ka iya samun wanda iya kansa mace biyu ko ɗaya ce za a iya samun daidaito. To anan idan shi mai jikin bai iya yi wa kansa adalci ba, ko kuma bai fahimci kansa ba, zai iya jawo rigimar da ta fi ƙarfinsa.

Ma’ana dai shi ne zai iya faɗa wa kansa gaskiya mata nawa ne zai iya zama da su bisa adalci.

ɓangare na ƙarshe, shi ne wanda mace ba ta dame shi ba, kuma shi ba za a kira shi marar lafiya ba. Zai iya kusantar mace, amma idan zai yi shekara bai kusanceta ba ba shi da damuwa.

A wannan gaɓar zan so in yi misali da wata ƙara da aka taɓa kawo min ba da jimawa ba, wata mata ce mijinta ya ce zai ƙara aure, anan sai ta yi ta faɗa, a tunanin mutane kishi ne, amma lokacin da ta yi bayani sai na fahimci cewa, mijinta na daga cikin irin waɗannan maza kashi na uku, domin sai ta yi daƙyar yake kusantarta, don haka a lokacin da ya ɗauko zancen aure, sai ta tsammaci ita ɗin ce dai ba ya san kusanta, don haka ta yi iya mai yi don sanin ko wata matsala take da ita da ya sa ba ya kusantar ta, amma ya ce babu abinda yake tare da ita da ba ya so.

Ta bi abokane da neman shawara, sun aza ta kan neman maganin ni’ima, ba wani canji, ta je asibiti, an tabbatar mata ba ta tare da wani nakasu ko matsala da ka iya sa mijin ya gujeta.

Daga ƙarshe dai ta yanke shawarar kawai ta rabu da shi, inda ta ce ta dai fahimci sonta ne ba ya yi.

Da na yi magana da mijin ya tabbatar min da shi haka yanayin shi yake, da na tambaye shi ya yake tunanin zama da mata biyu alhali ko guda ɗayan dakyar ake tafiyar, a mamaki na sai ya sanar da ni ai yana da wadatar da zai iya auren mata har uku, ya iya ciyar da su da tufatar da su ba tare da sun rasa komai ba.

Wannan na ɗaya daga cikin kuskuren da maza ke yi, da yawa suna kallon ci da sha kawai ne ake buƙata a gidan aure, ba sa tunanin idan shi kaɗai ne, to mai zai hana macen ta yi zamanta a gidan babanta ya ci gaba da ciyar da ita.

Idan har ana so a samu zaman aure na kwanciyar hankali, to fa sai an cire son rai tun a lokacin da ake shirin yin auren. Shin zan iya riƙe mata biyu? Zan iya ba su ci da sha daidai gwargwado? Zan iya ba wa kowacce daga ciki haƙƙinta na aure ba tare da na tauye wata ba? Zan iya kula da abinda za a haifa min ba tare da na zube wa titi su ba da zummar almajiranci? Shin zan iya adalci a tsakanisu? Kamar yadda ayar da muka kawo ta ambata, wato “Idan kun ji tsoron kasa adalci a tsakaninsu, to ku auri ɗaya.”

Duk wani a abokanen ka da zai zuga ka wai kan cewa, nuna ƙaramta ne, kowa ya yi ƙari a abokanen ka, ko har na ƙasa da kai sun ƙara, don haka rashin ƙarin naka gazawa ce, kada ka bari waɗannan maganganu su yi tasiri gare ka ka ƙaro aure don su, domin duk arzikin ka, zai iya yiwa akwai abinda ba za ka iya cikawa ba daga cikin ababen da muka ambata, don haka kai ne kawai za ka iya yi wa kanka adalci yayin ƙarin aure.

Aure sunnah ce mai ƙarfi, haka ma ƙarin aure, don haka ba inda zai iya zama laifi idan ka nemi ƙara mata komai biyayya da kyautatawar da matarka ke yi maka, matuƙar dai za a bi yadda Allah ya ce a yi.

By ukarofi