Daga UNCLE LARABI
An samu tattaunawa kan yadda ake yawan kama kayan ’yan kasuwar Sabon Gari tsakanin MD da SA da OC Task Force da kuma wasu daga cikin wakilan ’yan kasuwar Sabon Gari a ofishin DPO da ke Market Uut Post.
Alhamdulillah! An samu ƙorafe-ƙorafe daga bakin ’yan kasuwa kan yadda ake yawan kama musu kaya daga an fito da shi daga cikin kasuwa, musamman a waɗannan guraren da suka fi ƙaurin suna kamar haka; Rawul ɗin Bata da wajen ƙofar Abacha da wajen ’Yankura da Ibo Road-by-Market.
Hakan yana haifar da korar kwastomomi kuma babban koma-baya ne ga kasuwancin Jihar Kano.
Kasuwar Abubakar Rimi (wacce aka fi sani da Kasuwar Sabon Gari) ita ce kasuwa mafi girma da shahara cikin kasuwannin Kano da ake zuwa yin sarin kayayyaki daga dukkan sassan faɗin ƙasar nan har ma da ƙasashen da ke maƙotaka da mu na Afrika.
To, alhamdulillah, an gabatar da ƙorafe-ƙorafe, duk da babu lokaci sosai, amma dai an tattauna an kuma fahimci ƙasu daga cikin abinda ke haifar da matsalar da kuma yin alƙawarin insha Allahu daga ƙannan zaman kowanne ɓangare za su ɗauki gabaren gyaran.
A ɓangaren jami’an tsaro sun bayar da tabbaci samun tsaro a kasuwar, musamman yadda ake yawan samun sace-sace da kuma ɓalle shaguna ana yi musu sata. Sun bayar da umarnin Hana shigar yara masu buhu cikin kasuwar da sassafe. Sun ce ya kamata a dakatar da su har sai lokacin da mutane da yawa suka buɗe shagunansu. Sannan sun yi maganar buhun da suke shiga da shi ya kamata a ce su samu leda ‘transparent’ su dinga shiga da ita tunda kwali ko ledoji suke ɗiba ta yadda za a ga duk abinda yake cikin ledar, don samar da sauƙi ga yawan sace-sacen da ake yi.
Sai abu na gaba, OC Task Force ya yi magana akan kayan da suka yi ‘eɗpire’, wanda ake siyarwa a cikin kasuwar. Ya bayar da misali da alewa da biskit, wanda ana samun wasu mutanen masu son zuciya da kayan nasu ya yi ‘eɗpiring’ kuma suke siyarwa da mutane, wanda hakan zai iya cutarwa ko ya shafi lafiyar al’umma. Don haka don Allah kowa ya kiyaye wajen duba ‘eɗpiry date’ ɗin kayan da zai siyo ko da ba na ci ba ne ko sha.
An yi maganar Hukumar NAFDAC. ita NAFDAC a dokar ƙasa, Nijeriya ce ta ƙirƙire ta, kuma ta ƙirƙira ne, don ƙayan da ake ci ko ake sha, musamman kayan abinci ko magunguna. Shi ya sa ma aka kira ta da ‘Nigerian Agency for Food and Drugs’, amma ta wani ɓangaren an shigo da kayan da ake shafawa, wato su ne ‘cosmetics’, amma su kansu NAFDAC ba sa zafafawa akan kayan kwalliyar (cosmetics) sai lokaci zuwa lokaci sukan waiwaya kan kayan da suke ‘fading skin’ (sune kayan bleaching), saboda suna cutar da fata.
Saɓanin waɗannan kaya na ‘cosmetics’ masu canja launin fata, NAFDAC ba ta kallon sauran kayan kamar yadda jami’an tsaro na bakin kasuwa suke yawan tambayar ina NAFDAC akan ‘ƙueen Elizabeth Cocoa’ da kowa ya san ba ya ‘fading skin’.
Bari mu koma kan wasu batutuwan. Sun yi maganar masu ‘Islamic Chemist’. Su waɗannan a ƙa’ida ya kamata su samu NAFDAC ‘number’ tunda abu ne da ake sha kuma yana da kusanci da lafiyar mutum. Amma sai suka bayar da uzurin tunda NAFDAC tana wahalar samu, akwai wata cibiya ta ‘Center of Medicine’ a Jami’ar Bayero (BUK) da suke yi wa masu magungunan gargajiya gwaji da kuma ba su shaidar maganinsa zai iya Siyarwa da Al’umma. Don haka ya kamata duk masu wannan harkar su daure su mallaki wannan takardun don tsira da mutuncinsu a harkar kasuwanci tare da tseratar da lafiyar al’umma.
Sannan sun Yi magana akan cewar insha Allah idan suka ga Kaya suka duba ‘Eɗpiry date’ suka ga lafiya lau, to babu kuma wani abu da za su sake tambaya tunda ba kowa ne kaya ne dole sai ya mallaki NAFDAC ‘number’ ba, musamman kayan da ake yin su a ‘African Countries’, wanda muna da ‘collaboration’ na Kasuwanci tsakaninmu da su.
Sannan ko da kayan da ake siyowa daga ƙasashen ƙetare ne dole ita ƙasar da ta yi kayan Bata bari a fitar da kayan da ba su da inganci daga ƙasarta, don gudun durƙusar da cigaban kasuwancin ƙasar.
Daga ƙarshe muna yi wa Mai Girma MD, Abdul B. Hussain, MD kasuwar Sabon Gari, da SA na Gwamna da OC Task Force da DPO bisa sauraren ƙorafin ’yan kasuwa da suka yi, kuma suka bayar da lokaci aka zauna aka tattauna matsaloli tare da samar da matsaya akan za a ɗauki mataki wanda zai farfaɗo mana da kasuwancinmu na kasuwar Sabon Gari da Jihar Kano bakiɗaya. Ma’assalam!
Sunana Abdullahi Jibril ɗankantoma (Uncle Larabi), ɗan kasuwa mazaunin birnin Kano
