Daga MUHAMMAD AL-AMIN, Damaturu
Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga gwamnatin tarayya wajen yin amfani da kimiyya da fasaha a matsayin sabon salon yaƙi da ƴan ta’addan Boko Haram da masu garkuwa da jama’a a Nijeriya.
Shugaban jam’iyyar, ya bayar da wannan shawarar ne jiya Laraba, sa’ilin da ya jagoranci mambobin kwamitin gudanarwar jam’iyyar zuwa Jihar Yobe, domin miƙa saƙon jaje ga Gwamnan jihar, Mai Mala Buni, biyo bayan harin ta’addanci da Boko Haram su ka kaiwa sansanin sojoji dake Buni Gari, ranar Asabar da ta gabata.
Ganduje ya ƙara da cewa yaƙin da ake yi da ƴan ta’adda tare da masu garkuwa da jama’a, dole ne a fito da sabbin sauye-sauyen zamani na kimiyya da fasaha don samun nasara.
Ya ce abin takaici ne irin yadda ƴan ta’addan suke cin karensu babu babbaka a fadin ƙasar nan.
“Nijeriya ta na asarar makudan kuɗaɗe, waɗanda ya kamata a ce an yi amfani da su ne wajen ci gaban ƙasa, amma sakamakon matsalolin tsaro dasu ake amfani wajen sake gyara abubuwan da ƴan ta’adda suka lalata.
“Har ila yau kuma, a matsayin ku na shugabanni, an karkatar da hankalinku zuwa wasu al’amurra daban, inda hakan yake rage muku kuzari daga aiwatar da muhimman tsare-tsaren ci gaba.” In ji Ganduje.
A nashi ɓangaren, Gwamna Buni ya ce gwamnatoci a matakai daban-daban su na duba yiyuwar yadda za a yi amfani da fasahar zamani a yaƙi matsalolin tsaro .
“A matakin farko da kuma a Gwamnonin Tafkin Chad, mu na nazari sosai kan yadda waɗannan ƴan ta’adda suke amfani da jirage marasa matuƙa, don samun haɗin kai tare da hukumomin tsaro don magance wannan matsala.” In ji Gwamna Buni.
