
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Tsaron Nijeriya, Badaru Abubakar ya bayyana yadda iyakokin ƙasa ke fuskantar matsalolin hare-haren ƴan ta’adda da suka haɗa da mayaƙan Lakurawa da Mahmudawa.
Ya kuma tabbatar wa al’umma cewa gwamnati ta na iya ƙoƙarinta wajen ganin ta inganta tsaro a dukkan ɓangarorinsu.
A lokacin da ya ke magana a taron manema labarai na ministoci na shekarar 2025, Ministan ya bayyana ƙalubalen da ake fuskanta a fannin tsaro da kuma nasarorin da aka samu daga ɓangaren ƙoƙarin da dakarun tsaro suke yi wajen bai wa sassan Nijeriya kariya musamman akan kutse ta iyakokinta.
A yayin bada amsa game da halin tsaro a Jihohin Zamfara da Katsina, Ministan ya ce an samu ci-gaba ta fuskar buɗe wasu tituna da kasuwanni da aka rufe a baya sakamakon tasirin ayyukan ta’addancin ɓarayin daji da ƴan bindiga a Jibiya da Batsari.
Badaru ya bayyana cewa, sojoji suna ƙoƙarin ƙwato wasu ƙananan hukumomi da ke ƙarƙashin ikon ƴan ta’adda a jihohin.
Ya kuma ce, ƴan ta’addar ƙungiyoyin Lakurawa da Mahmudawa suna gudanar da harkokinsu a iyakokin, ya na mai cewa lallai sai dakarun sun sauya salo wajen daƙile ayyukan mayaƙan.
Ministan ya ƙara da cewa, akwai buƙatar a samu haɗin-gwiwa a mataki na ƙasa-da-ƙasa domin tabbatar da tsaro da ɗorewarsa acikin al’ummar Nijeriya a matsayinta na wadda ta fi kowace ƙasa yawan mutane a Afirka.
