Rikicin jagorancin ACF kan zargin biliyan 3.9 ya sa ‘yan sanda sun rufe hedikwatar ƙungiyar

Spread the love

Rikicin da ya dabaibaye Ƙungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) ya munana a ranar Talata, bayan da ’yan sanda suka rufe hedikwatar ƙungiyar da ke Kaduna gababin taron gaggawa na Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) da aka shirya.

Bayanai na nune da cewa, tun da misalin ƙarfe 7 na daren jiya Talata aka kulle Hedikwatar ACF da ke kan titin Sakkwato a cikin garin Kaduna, inda motocin ’yan sanda suka yi cincirindo a ƙofar shiga, a yayin da mambobin NEC ke shirin taron, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Rahotanni sun nuna cewa, mambobin NEC ƙarƙashin jagorancin Barista Mamman Mike Osuman, SAN, sun shirya taron gaggawa a hedikwatar a ranar, amma rikici ya hana hakan.

A cikin wata sanarwa da Osuman ya fitar mai taken “An mamaye Hedikwatar ACF”, ya zargi Shugaban Kwamitin Amintattu (BoT) na ƙungiyar, Alhaji Bashir Xalhatu, da yin abin da ya kura wuce iyakarsa bisa kundin tsarin mulkin ACF.

Ya ƙara da cewa shi da wasu jiga-jigan Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC) sun maƙale a cikin hedikwatar, lamarin da ya kira da “tauye haƙƙi.”

Sai dai a wata sanarwa daban, Alhaji Bashir Ɗalhatu, wanda tsohon minista ne kuma Wazirin Dutse, ya bayyana taron a matsayin ba bisa ƙa’ida ba, yana mai cewa Malam Murtala Aliyu, sakataren ƙungiyar kuma tsohon minista, ba shi da hurumin kiran taron, domin wa’adinsa ya ƙare.

Kakakin rundunar, DSP Mansur Hassan, ya ce: “Ba su rufe ofishin ba, abinda ya faru shi ne sun samu wasiƙu biyu da bayanan sirri cewa ɓangarorin na shirin gudanar da taro a halin yanzu Jihar Kaduna na cikin zaman lafiya, kuma ba za su bari a samu rikici ba.”

Rikicin da ya kunno kai a ACF ya ta’allaqa ne kan shugabanci da kuma rawar da NEC da BoT ke takawa.

By Babaji