Daga JOHN D WADA a Keffi
Cibiyar nazarin jinsi ta jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, tare da haɗin gwiwar sashen kimiyar fasa’a (ICT) na jami’ar da kuma shirin wayar da kan jama’a kan kiwon lafiya na 2026 sun buƙaci a ƙara himma da ƙoƙarin wajen bai wa mata dama a fannin fasa’a da sadarwa (ICT) domin inganta harkokin kiwon lafiya da ci gaba mai ɗorewa.
Taron ya gudana a babban ɗakin tarurruka na jami’ar kwanan nan inda aka tara manyan masu ruwa da tsaki da ƙwararrun kiwon lafiya da masana ICT don tantance yadda sabbin fasahohi za su inganta lafiya da haƙƙi da damammakin mata musamman ɗalibai.
Shugabar jami’ar jihar Nasarawa Farfesa Sa’adatu Hassan Liman wacce darakta na cibiyar kasuwanci, Farfesa Rashida Olarewaju ta wakilta, ta yaba da shirye-shiryen cibiyar nazarin jinsi. Ta bayyana haɗin gwiwar da sashen ICT a matsayin alamar haɗin kai a cikin jami’ar da kuma jajircewa kan ci gaba mai ɗorewa.
Ta ce “Wannan haɗin gwiwa yana nuna ƙarfin aiki tare domin cimma buri guda. Yana tabbatar da cewa haɗin gwiwa zai iya kawo canji mai ma’ana da ɗorewa,” ta ƙara tabbatar da aniyar jami’ar kan ƙirƙire-ƙirƙire, haɗa kai da walwalar ɗalibai.
Da take jawabi a madadin sashen ICT, Misis Hajara J. Garba wacce ta wakilci Darakta, Farfesa Nachamada Vachaku Blamah ta sake jaddada aniyar sashen na baiwa mata ɗalibai horo kan fasaha da jagoranci da samun kayan aikin fasaha. Ta jaddada muhimmiyar rawar da ICT ke takawa a harkokin kiwon lafiya na zamani.
“Fasaha ta zama ginshiƙin kiwon lafiya daga ayyukan sadarwa ta zamani da ke kaiwa yankunan karkara zuwa manhajoji na waya da ke tallafa wa kula da lafiyar mata masu juna biyu da tsarin bayanai da ke ƙarfafa martani kan kiwon lafiya na jama’a da sauransu “. ta bayyana.
Haka shima sakataren dindindin na ma’aikatar kiwon lafiya ta Jihar Nasarawa, Dr. Ibrahim Adamu wacce Dr. Alhassan Adamu ya wakilta ya sake tabbatar da aniyar gwamnati kan kiwon lafiyar matasa da samun ingantaccen bayanin kiwon lafiya.
Ya tabbatar da ci gaba da goyon baya ga shirye-shiryen da ke ƙarfafa mata su rayu cikin lafiya da amfani.
A saƙon fatan alheri, Sarkin Keffi, Dr. Shehu Chindo Yamusa III, wanda Wanban Keffi ya wakilta ya yaba wa masu shirya taron saboda haɗa ICT da wayar da kai akan kiwon lafiya yana bayyana shi a matsayin tsari mai cikakkiyar ma’ana na ci gaba da ke renon tunani da lafiyar jiki baki ɗaya.
Darakta na cibiyar nazarin Jinsi, Dr. Comfort Adokwe-Obed tare da mataimakiyar darakta (Ilimi), Dr. Ochanya Mercy Yakubu Lamai sun jaddada buƙatar bai wa mata horo kan fasaha da suke buƙata domin yin nasara a duniyar fasaha ta yau.
Sunce wannan shiri ya dace da ƙoƙarin duniya na inganta daidaiton jinsi da ƙara yawan shigar mata a fannin kimiyya da ƙirƙire-ƙirƙire.
Taron ya ƙunshi jawabi daga Mary Jane Sule kan “Amfani da ICT wajen inganta lafiyar matan matasa, hakkokinsu da damammakinsu a Najeriya,” da Aisha Musa Abubakar kan “Inganta lafiya da walwalar matan matasa a zamani na fasaha.”
An kuma gudanar da tattaunawa ta kwamitin masana mai taken “Hada Matan Matasa da Fasaha: Kayan Aiki na Ilimin Kiwon Lafiya da Karfafa Karfi,” inda masana kamar Dr. Lamai, Dr. Adaeze Ezeil, Dr. Faith Awadzi Albert, Yunus Fatima Abdulsalam, Dr. Abdullahi Rabo, da Dr. Asaniyan Samson suka halarta.
Daga cikin fitattun abubuwan da aka gudanar a yayin taron akwai gasar kacici-kacici na tambayoyi tsakanin makarantun da suka halarta inda makarantar St. Peters Anglican ta fito a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka ci nasara tare da wasu makarantu biyu.
An kammala taron da godiya daga Dr. Hajara Ahmed II, mataimakiyar darakta na shirye-shirye a cibiyar nazarin jinsi, yayin da aka bai wa makarantun da suka ci nasara kyaututtuka daga hannun Darakta, Dr. Adokwe-Obed da sauransu.
