Daga JOHN D WADA a Lafia
Ma’aikatan hukumar kula da harkokin ƙananan hukumomin jihar Nasarawa wato local government service commission (LGSC) a turance sun yaba wa shugabansu Alhaji Aliyu Mustapha Abdullahi dangane da ire-iren kyawawan shirye-shiryensa da yake aiwatarwa a hukumar da a cewarsu zuwa yanzu cikin shekara guda kacal an samu ɗimbin cigaba masu ma’ana a hukumar.
Ma’aikatan hukumar sun bayyana ra’ayinsu ne a lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu a jihar John Wada don jin ra’ayin nasu game da salon shugabancin shi Alhaji Aliyu Mustapha Abdullahi cikin shekara ɗaya da ta gabata.
Sunce tabbas dole su cigaba da yaba wa Alhaji Aliyu Mustapha Abdullahi musamman Idan akayi la’akari da yadda yake tafiyar da harkokin hukumar dake kula da harkokin duka ƙananan hukumomin jihar 13 kawo yanzu cikin mutunci da riƙon amana da kuma uwa uba yadda yake haɗa kawunan duka ma’aikatan hukumar waje guda don cimma buri da manufar ma’aikatar a duka fannoni tun zuwansa a shekara ɗaya.
Ma’aikatan da aka gana da su sun bayyana wasu daga cikin ɗimbin ayyukan cigaba da shi shugaban na su Alhaji Aliyu Mustapha Abdullahi ke yi kawo yanzu cikin shekara ɗaya kacal cewa sun haɗa da warware wasu rigingimun cikin gida da na waje da suka shafi harkokin ƙananan hukumomi 13 a jihar da haɗa kan shugabannin ƙananan hukumomin da tabbatar da kyawawan dangantaka tsakanin ƙananan hukumomin da gwamnatin jihar ta Nasarawa da tabbatar ana biyan duka haƙƙokin ma’aikatan a fannin albashinsu da alawus din su da inganta tsarin ayyuka a ma’aikatan inda a yanzu duka ma’aikatan ke aiki tuƙuru tare da sauransu saɓanin yadda lamarin yake a da kafin zuwansa.
Sun ƙara da cewa Alhaji Aliyu Mustapha Abdullahi ya shirya zama na musamman tsakanin duka ma’aikatan da shi kansa inda yake ƙarfafa musu gwiwa game da buƙatar aiki tuƙuru don cimma burin ma’aikatan tare da turosu tarurrukan sanin makaman aiki don faɗaɗa ƙwarewarsu da sauransu.
Ma’aikatan hukumar kula da harkokin ƙananan hukumomin jihar da aka zanta da su sun yi amfani da damar inda suka yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da abinda suka bayyana a matsayin zaɓi nagari da yayi na naɗa shi shugaban nasu alhaji Aliyu Mustapha Abdullahi a muƙamin inda suke ce tabbas zuwa yanzu kam kwalliya na cigaba da biyan kuɗin sabulu don a yanzu bincike ya tabbatar ba a taba yin shugaba nagari mai kuma kirki da tsari kamar Alhaji Aliyu Mustapha Abdullahi a hukumar ba.
Da aka tambayesu wanna kira na musamman suke da shi wa shugabansu Alhaji Aliyu Mustapha Abdullahi sai duk suka bayyana cewar tabbas suna kira a gareshi ne ya cigaba da waɗannan kyawawan sadaukarwa da yake yi wa al’ummar jihar baki ɗaya musamman yankunan karkara ta hukumar don Allah ne kawai zai saka masa da alheri kana a nasu ɓangaren kuma sunyi alƙawarin cigaba da bashi cikakken goyon baya da yi masa biyayya don bashi damar cigaba da gudanar da ire-iren kyawawan ayukan cigaban da yake yi a ma’aikatar kawo yanzu.
A ƙarshe wakilinmu ya kuma ruwaito cewa shi dai shugaban ma’aikatar dake kula da harkokin duka ƙananan hukumomin jihar 13 dake birnin Lafia fadar gwamnatin jihar wato Alhaji Aliyu Mustapha Abdullahi na ɗaya daga cikin wasu shugabannin wasu mahimman hukumomin gwamnatin jihar da gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule ya naɗa su muƙaman daban-daban wanda daga bisani majalisar dokokin jihar ta tabbatar da naɗin nasu suka fara aiki shekara ɗaya da ta gabata kenan a 2025.
