
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Zakari Umoru, ɗaya daga cikin mutane shida da aka gurfanar a Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin hannu a kitsa kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, ya ce wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma ne suka ruɗe shi akan al’amarin.
Rahotanni sun bayyana cewa, Umoru, wanda ma’aikacin Kamfanin Julius Berger ne, an tura shi aiki ne a sashen kulawa na Fadar Shugaban Ƙasa, inda ya yi wannan iƙirari a wani faifan bidiyo da aka haska akan idon Mai Shari’a Joyce Abdulmalik.
Haka kuma, shi ne na huɗu cikin waɗanda Gwamnatin Tarayya ta shigar da ƙarar cin amanar ƙasa akan su.
Ya bayyana cewa, al’amarin ya faru ne a watan Mayu, 2025 ta wanda ake tuhuma na uku, wato wani mai suna Sufeto Ahmed Ibrahim, wanda ke aiki da asibitin fadar.
A cewarsa, Ibrahim ne ya gabatar masa da wani mai suna Hassan Mohammed, wanda daga bisani ya bayyana a matsayin “Kanal Mohammed Ma’aji”, wanda kuma ya yi ɓadda kama na wanda zai yi masa aikin wutar lantarki a wani gida da ake ginawa.
Ya ce, da fari ya ɗauka Ma’aji ɗan kasuwa ne, musamman bayan karɓar kuɗi da asusun bankin da ke amsa sunansa a lokuta mabanbanta.
Umoru ya ƙara da cewa, ya sha karɓar kuɗi ta asusun banki daga Ma’aji, inda a wasu lokutan hakan na faruwa ne a gaban Sufeto Ibrahim.
Kazalika, ya yi bayanin ziyarce-ziyarce daga Ma’aji tare da wani abokinsa mai suna Usman, wanda shi ma daga bisani ya gano cewa jami’in soja ne.
Har ila yau, a faifan bidiyon an ga hujjar da ke zargin Ma’ajin da ba wa Umoru jakar “Ghana Must Go” cike da kuɗaɗe a ranar 24 ga Satumba, 2025.
A yayin ɗaukar bayanai, Umoru ya ce ya taɓa kama Usman yana ɗaukar hotuna a ofishinsa, inda ya gargaɗe shi akan aikata irin haka, yana mai cewa bai taɓa sanin cewa ana kitsa makircin juyin mulki ba ne, inda ya tirje akan cewa Sufeto Ibrahim ne ya ruɗe shi.
