Rikicin Smith da Chris: Oscar Award sun dakatar da Smith shekaru 10

Daga AISHA ASAS

Hukuncin da mahukunta suka sha alwashin ɗauka kan jarumi Will Smith game da labta wa Chris Rock mari a bainar jama’a, a ranar bikin karramawa na Oscar Award ya bayyana, inda ƙungiyar ta haramta wa Smith halartar taro irin wannan da ma takwarorinsa na tsawon shekaru goma.

A ranar Juma’ar nan da ta gabata ne, masu alhakin shirya gagarumin bikin bayyar da kyauta na Oscar wato Academy of Motion Pictures Arts and Sciences suka bayyana abin da Smith ya aikata a matsayin abin da ba a lamunta da shi ba, kuma ba zai tafi ba tare da hukuntawa ba.

A wata takarda da mambobin ƙungiyar suka fitar ta bayyana cewa, jarumin wanda ya samu nasarar cin lambar yabo a karon farko na rayuwarsa, an haramta ma shi halartar kowanne taro da wannan ƙungiya za ta shirya har na tsawon shekaru goma.

“Wannan hukumci da mu ka yanke a yau, mataki ne na kariya ga masu ƙayatar da taron da ma mahalarta taron a koda yaushe tare kuma da maido da ƙima da darajar wannan ƙungiya,” Inji ƙungiyar.

A ɓangaren wanda wannan hukuncin ya hau kan sa, jarumi Will Smith ya karɓi hukuncin da hannu biyu ba tare da ja ko ƙorafi ba, inda yake cewa, “Na yarda kuma na amince da hukuncin da ƙungiyar ta yanke kaina.”

Jarumi Smith dai ya dirar wa ɗan wasan barkwanci Chris ne a inda yake tsaye yana nishaxantar da mahalarta taron, ba zato ba tsammani ya sharara masa mari, wannan ya biyo bayan yin raha da kan matar Smith, Jada Pinkett Smith, wanda yake xauke da askin kwashe duk. Smith bai ɗauki abin a matsayin raha ba, kasancewar matar tasa na fama da cutar fata mai suna ‘alopecia’, wadda ta zama silar zubewar gashin kanta. Bayan wannan aika-aika da Smith ya yi ga Rock, ya koma wurin zamansa yana mai aiken zagi ga abokin sana’ar tasa da ya mara.

Wannan al’amari dai ya jawo cece-kuce ciki da wajen masana’antar finafinai ta Hollywood, inda aka samu rarabuwa da kuma mabanbantan ra’ayi kan lamarin. Wasu na ganin laifin Jarumi Smith da tir da ɗanyen hukuncin da ya yanke. Sai dai wasu suna kallon abin a matsayin ajizanci na ɗan Adam, a cewarsu, ba wanda zai iya jure cin zarafin wanda yake so.

Sai dai a ɓangaren ƙungiyar, sun bayyana jin haushin su da kuma kallon abin da Smith ya yi a matsayin rashin girmama taron da kuma ita kanta duniyar barkwanci, don haka suka sha alwashin zama a ranar 18 ga watan Afrilu, don yanke hukunci kan wannan al’amari. Sai dai kafin kai wa ga wannan lokaci, jarumin ya riga malam Masallaci ta hanyar fice wa daga ƙungiyar, ya kuma kira abin da ya aikata a matsayin abu mai matuƙar ciwo kuma laifi ne da ba shi da wata hujjar kare shi.

A lokacin da jarumin ya karɓi kambun karramawa da ya ci da fim ɗin da ya fito mai suna ‘King Richard’, ya bayar da haƙuri kan ɗanyen aikin da ya yi. Ya kuma yi aiken saƙon ban haƙuri ga Chris ta kafar sada zumunta.

Shi kuwa ɗan wasan barkwancin da aka mara, ya yi gum da bakinsa tun lokacin da al’amarin ya faru zuwa yanzu, ma’ana dai ya ƙi ya ba wa mutane damar sanin ra’ayi da matakin da zai ɗauka. Sai dai ya bayyana cewa har yanzu yana ƙoƙarin sarrafa abin da ya faru a ranar. Ya faɗi hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a ‘crowd at a comedy show’ a satin da ya gabata.

“A jawabin da mu ka fitar, ba mu samu yin gamsashen bayani kan lamarin ba, don haka muna bayar da haƙuri kan hakan. Mun yanke wannan hukunci ne don ya zama izna ga sauran ‘yan ƙungiyar har ma da mahalarta. Mun yi takaici da jin kunyar faruwan wannan lamari.” ƙungiyar ta bayyana a takardar da ta fitar.

ƙungiyar ta bayyana cewa, Smith ya ƙi ya bar wurin taron bayan ya wanke Chris da mari, duk da cewa babu tabbacin an nemi hakan daga gare shi.

Jami’an tsaro sun yi yunƙurin damƙe jarumin bayan faruwar lamarin, sai dai Chris Rock ya nuna dadako ta hanyar hana faruwar hakan, a cewar wani darakta.