Rubutu makaranta ce babba, inji Kabiru Jammaje

“Ina da burin samar da abin da za a riƙa tunawa da ni”

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano 

Idan ana maganar matasan da suka bayar da gudummawar su a duniyar marubutan littattafai da kuma yaɗa ilimi a cikin jama’a, to kuwa za a iya saka Kabiru Musa Jammaje a sahun gaba. Domin kuwa shi marubuci ne wanda ya fita daban a cikin marubutan da mu ke da su a ƙasar nan. Domin kuwa baya ga littattafai masu yawa da ya rubuta, ya yi amfani da damar in da faɗaɗa rubutun na sa zuwa aji na koyar da darasin Turanci domin ilmintar da jama’a yaren Turanci. A cikin tattaunawar da mu ka yi da shi, ya bayyana yadda ya fara rubutun da kuma samar da makarantun ajin Turanci tun daga Kano har zuwa wasu jihohi na Arewa. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance:

MANHAJA: Kana cikin marubutan da suke rubutu da harshen Turanci a Ƙasar Hausa wanda rubutun na ka ya kai ka ga samar da makarantun koyar da harshen Turanci. Za mu so ka yi wa masu karatu bayanin yadda ka faro harkar rubutun.
JAMMAJE: To na fara harkar rubutun ne a shekarar 2001, na rubuta littafi na na farko Difandivil Ingilish, wanda a lokacin ma na yi shi wani ɗan ƙarami ne na sakawa a aljihu, to kuma bayan da aka buga shi ya shiga kasuwa, ganin ya karɓu sai kuma na rubuta wani na Turanci mai fassara da Hausa mai suna ‘New of Learning’, to 20003 kuma sai na rubuta ‘New way’ shi ma mai fassarar Hausa. Tun daga lokacin dai sai na shiga rubutun gadan-gadan, kuma alhamdulillahi littattafan sun samu karɓuwa a kasuwa sosai.

To baya ga rubutun littafai an san ka a koyar da Turanci wanda a yanzu kai ne mai Makarantar koyar da Turanci ta Jammaje Academy ko me ya bambanta makarantar da kuma Littafin?
To ai kusan tare su ke, domin mai rubutu ai karanwata yake yi. Kuma duk lokacin da ka zo kana rubutu kana faɗa koyarwa ne, don haka rubutu kansa makaranta ce babba, dalilin kenan da ya sa ban samu wata wahala wajen haɗa rubutun da koyarwa ba .
Kuma ita koyarwar na fara ta ne tun lokacin da na zo Kano da zama, domin kafin wannan lokacin ina garin Jammaje ne da ke ƙaramar Hukumar Tudun wada a nan ne mahaifata. Amma nan garin kano dangin mahaifiyata ne a Unguwar Ayagi, don haka da na dawo Kano da zama a shekarar 2002 to a lokacin mutane da suke zaune a unguwa, nan Unguwar Aisami suke zuwa su same ni har gida na koya musu karatu. Don haka sai suka fara zuwa muna yin karatun a gida.

Sai dai da mutane suka ci gaba da zuwa sai aka fara yawa, don haka sai na ga abin ba zai yiwu ba wajen ya yi mana kaɗan, daga nan sai mu ka koma makarantar firamare ta Ɗandago in da mu ka samu aron aji guda biyu mu ke yi.

Amma dai tun kafin na fara wannan tun ina Jammaje na buɗe ajin koyar da matasa, inda na ke koya mu su yadda za su yi amfani da yaren Turanci. In dai ban manta ba na yi wannan koyarwar ne a 1996, saboda a shekarar na kammala sakandire. Ina gamawa kuma na buɗe na fara koyar da su, amma dai a nan Kano, mun fara ne 2003, sai kuma a 2004 zuwa 2005 mu ka koma makarantar Aminu Kano ‘Commacial College’ kuma komawar mu wannan waje ta ba mu damar kafa makarantar Jammaje Academy a shekarar 2007, a lokacin mu ka sanar da duniya wadda a yanzu kowa ya san ta a duk faɗin ƙasar nan saboda mun yi fice a wajen koyar da Turanci. 

To bayan bunƙasar makarantar sai kuma ya zama an samar da rassa a wasu Unguwanni da wasu jihohi, ko ya aka yi wajen faɗaɗawar?
To lokacin da mu ka buɗe Jammaje English a nan Kano, mutane ba su ma fahimci yadda tsarin makamatar yake ba, amma dai ɗaliban farko da mu ka fara da su abin ya yi mu su tasiri don haka suka rinƙa jawo wasu. Don haka sai aka rinƙa mana waya a na neman ƙarin bayani, to a nan sai kuma wasu su ke ganin wajen ya yi mu su nisa, to muna tafiya a haka dai sai a yanzu ne mu ka samu damar faɗaɗawar .

To, ko me ya jawo jinkirin buɗewar sai a yanzu?
Ina ganin a lokacin shirin da mu ke yi bai kammalu ba, amma dai abin da ya jawo buɗewar mu a wannan lokacin abu biyu ne, na farko, lokacin da aka shiga zaman gida na Korona, sai na yi wani tsari na karatu daga gida wanda a ke kira ‘E-learning’ wanda mutane daga jihohi na Nijeriya suka rinqa shiga makarantar to sai na ga cewar idan har mutane kamar goma daga Birnin Kebbi za su shiga tsarin ‘E-learning’, idan na je har garin su na kafa in sha Allah mutane ɗari za su shiga, don haka sai na fara tunanin ya za a yi na je garuruwan su na kafa.

To ana cikin haka sai na karanta tarihin wani Bature ɗan Amurka shi yana da ‘online Store’ ne wanda duk abin da kake so za ka saya ne ta ‘online’ sunan ‘online’ ɗin nasa Amazon, kuma duk inda kake a duniya za ka iya sayayya daga Amazon kuma duk abin da kake so za ka iya saya. Kuma ɗan ƙaramin ‘Store’ ne ya fara da shi a Amruka sai ya zama a yanzu ya bunƙasa duk duniya yanzu, don haka sai na ga na samu abubuwa guda biyu da za su zaburar da ni na kafa rassan makarantar tun da idan mutum yana Amruka, amma duk duniya tana hannun sa, to ni kuma Arewacin Nijeriya zai yi mini wahala? Don haka sai na yi amfani da wannan damar tun da shi ma wacan Baturen mutum ne ƙwaƙwalwa ce da shi irin tamu, kuma duk mutum, mutum ne. 

Allah bai ɗaukaka shi ba sama da mu. Saboda haka in dai mutum zai yi wani ‘Store’ ya rinƙa kasuwanci da shi a duk duniya, mu kuma me ya sa ba za mu iya samar da Jammaje Academy a duk jihohin Arewa ba. Don haka sai na samu ƙarfin gwiwar farawa. Matakin farko daman mun samar da shi a Kaduna, daga nan sai mu ka tafi Jigawa mu ka buɗe a Dutse, daga nan mu ka tafi Katsina, kuma lokacin da muka fara a jihohin sai mu ka ga kamar mutane ba za su zo ba, amma daga baya sai ga shi suna zuwa da yawa.

To ganin Kano ba ta ƙoshi ba mun fara fita waje, don haka sai mu ka dawo mu ka buɗe rassa a unguwannin Kano in da mu ka fara da Tarauni, sai kuma Unguwar Dakata, kuma sai a farkon shekara a watan Janairu mu ke sa ran mu buɗe a Zoo Road da kuma Mil Tara, kuma daman babban Ofishin mu yana Kabuga, don haka zai zama mu na da rassa biyar a cikin garin Kano, don haka zai zama duk wanda ya ke Kano zai zama akwai wajen da ya fi kusa da shi, kuma Karatun Asabar da Lahadi ne kawai mu ke yi. Amma duk da haka ba mu tsaya a cikin ƙwaryar Kano ba, don mun shiga ƙananan hukumomi, mu ka samar da makarantar a Rano, Bichi da ɗanbatta.

Baya ga yaren Turanci muna koyar da abin da ya shafi harkar fim wato ‘Acting Class’ don samar wa da matasa aikin yi wanda ko a kwanakin baya ma, mun yaye ɗalibai da suka koya. 

Kuma kada ka manta Jammje Academy ta shirya finafinan Turanci Kamar ‘There’s a way’, ‘Light and Darkness’. ‘This is th way’, da kuma ‘In Search of th King’. 

Ko akwai wani burin da kake son ka cimma a harkar rubutu da koyarwa?
Eh, gaskiya haka ne. Domin ina son na yi yawo a duniya, domin Ita maƙarin ilimi ce. Kuma alhamdulillahi a yanzu na je ƙasashen duniya da dama irin su South Afirca, Zimbabwe, Kenya, Tanzania Rwanda, Ghana, Ivory Coast, Ethiopia, India, Saudi Arabia, Dubai, England, Turkey. Kuma Ina son na samar da wani abu da za a rinƙa tunawa da ni. Saboda Manzon Allah S A W, ya ce, “Mafi alherin ku shi ne wanda yake amfanar da mutane.” don haka ina son na zama ina da wannan don haka Ina son a rinqa tuna ni a matsayin wanda ya amfanar da mutane, ya samar mu su da aikin yi.


Sai kuma buri na biyu da na ke da shi, Ina son na zama Minista Ilimi (Dariya) Ina ganin waɗannan abubuwan da na ke yi idan aka gani za su zama su za a kalla a ga na cancanta da wannan matsayin idan Allah ya yarda. 

To, mene ne saƙon ka na ƙarshe? 
Ni saƙon da na ke da shi na ƙarshe, shi ne, mutane su sani cewar, su na buƙatar ilimin nan, don haka mu ba yaren Turanci kawai mu ke koyarwa ba duk da kowa ya san Turanci yare ne na duk duniya don haka ana buƙatar sa a duk abin da za ka yi, to ban da wannan kuma a reshen mu na Kabuga muna koyar da ‘General Knowledge’ kamar a koya ma ka wani abu na tarihi da wani abu na kimiyya da tsarin gudanar da gwamnati da tattalin arziki da sauran su.

To, madallah mun gode.
Ni ma na gode ƙwarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *