Rundunar ‘yan sanda ta fara farmaki a dazuzzukan Nasarawa domin kakkaɓe maɓoyar ‘yan bindiga da masu garkuwa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafia

Rundunar ‘yan sandan Jihar Nasarawa ta fara wani samame na musamman domin fatattakar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da makami da sauran miyagu dake ɓuya a cikin dazuzzuka a faɗin jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Shetima Mohammed Jauro ne ya ƙaddamar da aikin a ranar Laraba a Lafia yayin da yake jawabi ga jami’ai kafin su shiga dajin Alagye da ke ƙaramar hukumar Doma.

A cewarsa an ƙaddamar da aikin ne bisa umarnin sufeto janar na ‘yan sanda na ƙasa IGP Olatunji Disu domin ƙarfafa tsaro dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.

Ya bayyana cewa an tura tawagar jami’an dabara da masu yaƙi da garkuwa da mutane da jami’an leƙen asiri zuwa wuraren da aka gano suna da hatsari da kuma dazuzzukan da ake zargi.

Ya ce aikin zai cigaba har zuwa ƙarshen watan Disamba tare da umartar jami’an da su nuna ƙwarewa da bin ƙa’idojin aiki yadda ya kamata.

Domin tabbatar da ingantaccen tsari, CP ɗin yace an raba jihar zuwa sassa uku na aiki.

Sashi na A wanda ya ƙunshi yankin Lafia na ƙarƙashin ACP Lamidu Alƙali da Kwamandan Mopol 58, Lafia, Sashi na B wanda ya kunshi yankin Akwanga na ƙarƙashin ACP Kadir Umar, Kwamandan Mopol 38, Akwanga, yayin da Sashi na C wanda ya kunshi yankin Keffi ke ƙarƙashin ACP Olobekga Saligo da Kwamandan Mopol 69, Toto.

Ya kuma bayyana cewa mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ayyuka, DCP Sanusi Jidda, ne zai jagoranci ayyukan a dukkan sassa ukun domin samun nasarar rushe sansanonin miyagu.

Mohammed ya yi kira ga mazauna jihar da su rika bayar da sahihan bayanai kan lokaci game da motsin da ake zargi, yana mai tabbatar musu da cewa za a kula da irin waɗannan bayanai cikin sirri.

Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bin doka da oda tare da gudanar da harkokinsu na halal, yana mai jaddada ƙudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyi.

Da yake magana daga Dajin Alagye, DCP Jidda ya ce rahoton sirri ya nuna cewa dajin na amfani a matsayin mafakar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Jidda yace za a mika samamen zuwa wasu dazuzzukan jihar da nufin rushe sansanonin miyagu da kuma kama waɗanda ake zargi domin gurfanar da su a gaban kuliya.

“Ba za mu kyale wani ɗan daba ko mafakarsa ba. Mun fara gudanar da samame mai ƙarfi a dukkan sansanonin miyagu da aka sani da waɗanda ake zargi,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro na ta sintiri a cikin dazuzzuka kuma za su miƙa aikin zuwa dazuzzukan da ke ƙaramar hukumar Akwanga da Toto.

Yace an tura tawagar jami’an tsaro sama da rukuni shida ɗauke da kayan aiki masu kyau domin gudanar da aikin kuma a shirye suke su fuskanci miyagun da ke aiki a cikin dazuzzuka.

Jidda ya nuna ƙwarin gwiwar cewa cigaba da gudanar da ayyukan tsaro zai inganta tsaro tare da dawo da ƙwarin gwiwar jama’a a jihar.

By ukarofi

Leave a Reply