Rundunar ‘yan sandan Kano ta ƙaddamar da motocin aiki 22

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ƙarƙashin jagorancin CP Mamman Dauda ta ƙaddamar da motocin aiki ƙirar Helux guda 22 da sanatan Kano ta Arewa da ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa suka ba su don bunƙasa harkokin tsaro a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Da yake karɓar motocin a hedikwatar rundunar ta Kano, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Mamman Dauda ya yaba da irin wannan yunƙuri na waɗannan jagorori wajen irin abubuwan alkhairi da suke yi wajen inganta tsaro a jihar Kano.

Mamman Dauda ya bayyana godiyarsa ga Babban Sufeton ‘Yan Sanda na ƙasa, Usman Alkali Baba, bisa sahalewa da ya yi na inganta tsarin “Community policing” a jihohin ƙasar nan dan sa ido da yin duk mai yiwuwa wajen taikama wa jami’an tsaro a jihar Kano, tare jinjina wa Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, bisa ƙoƙarinsa na taimaka wa ɓangaren tsaro.

Kazalika, Kwamishinan ya yaba wa sanatan Kano ta Arewa, Sanata Barau I Jibrin da ɗan takarar kujerar majalisar tarayya, Mustapha Bala Dawaki bisa yunƙurin samar da ingantaccen tsaro a Kano.

Sanata Barau I Jibrin da Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Mamman Dauda yayin ƙaddamar da motocin a hedikwatar rundunar da ke Kano.

Shi ma a nasa jawabin yayin taron, Sanata Barau I Jibrin ya bayyana wa manema labarai cewa ya yi hakan ne kasancewar mazaɓarsa tana iyaka da jihar Katsina, kuma ana fama da matsalar tsaro a yankin, don haka ya yi tunanin samar da waɗannan motoci don kawo ɗauki da bunƙasa harkokin tsaro a yankin don magance matsalolin.

Haka zalika, Sanata Barau ya ce su ma sauran ‘yan sandan jihar Kano akwai shiri na musamman wajen bai wa kowane jami’i banur don ƙara inganta tsaro a faɗin jihar.

By Editor