Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Dangote

Spread the love

Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Alhaji Aliko Dangote, don Allah don Annabi S.A.W ina mai neman alfarma a gareka ka taimaka ka saka bakin akan maganar waƙar da (ADDT) Yusuf Balarabe ya sa na yi wa daribobin Dangote bayan na kashe kuɗi da ɓata lokaci amma duk ba a duba wannan ba ina da tabbacin mai gida baka san wannan magana ba, domin kuwa da kasan haka da za kai magana domin a yi min adalci.

Tabbas ni masalaha nake nema domin ba zan tava iya sharia da wannan kamfani ba, musamman idan natuna da alaƙar da ke tsakaninmu cewar yankinmu ɗaya ƙabilarmu ɗaya yaranmu ɗaya garinmu ɗaya addininmu daya ɗan uwa kake a gare ni, don haka nake naiman alfarma a gareka kataimaka ka saka baki domin a yi min adalci tsahon shekara 4 da yin wannan waƙa kuma ana matuqar amfani da ita a wannan kamfani na yi qorafi a rubuce lauyoyi sun shiga wannan magana domin su yi mana sulhu amma har yanzu shiru.

Duba da hujjojin da na taka ina fatan za ai min adalci.

Na gode Allah ya ƙara arziki da ɗaukaka.

Nuhu Ana Haka (Hausa musician), 08069554146/09015368057.

By Editor