IMF ta nemi gwamnatin Nijeriya kan ta cire tallafin mai kafin nan kafin tsakiyar 2023

Spread the love

Daga AMINA YUSUF ALI

Gidauniyar Kuɗi ta ƙasashen duniya, IMF ta nemi gwamnatin Nijeriya a kan ta cire tallafin mai kafin nan da tsakiyar shekarar da muke ciki ta 2023, sannan ta karkatar da kuɗin wajen gudanar da abubuwan cigaba.

IMF ta ce ta yi wannan kira ne saboda Nijeriya ta cika maganarta da ta ce za ta cire tallafin man a tsakiyar shekarar 2023.

Gudauniyar wacce take a Washington ta Amurka a wani rahoto da ta saki ranar Larabar makon da ya gabata ya bayyana cewa, ƙasar Nijeriya ta samu matsalar tattalin arziki bayan annobar COVID-19 tare da qari da tsadar man fetur da kuma almubazzarancin kuɗi.

Gidauniyar ta bayyana cewa, akwai buƙatar ɗaukar matakan da za su taimaka wajen fitar da ƙasar daga halin ƙaƙa-nika-yi da kuma basussuka.

Hakan ya sa suka nemi gwamnatin da ta cire tallafin man a tsakiyar shekarar 2023, ta kuma ƙara ƙaimi wajen zuba kuɗi a cikin abubuwan da suka kamata.

Domin a cewar IMF an samu
tazar sosai a tsakanin kuɗin haraji da jimillar kuɗaɗen da gwamnati ta kashe a shekarar 2022, a sakamakon hauhawar farashin tallafin man.

Wannan kuma a cewar su shi ya bayu ga samun tashin farashin canjin kuɗi a shekarar ta 2022.

Hakazalika, IMF, ta bayyana muhimmancin dagewa da harkar noma da kiwo saboda samar da ayyukan yi ga mutane, da kuma abinci.

By Editor