Shin canjin kuɗi ya cimma buri?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Kama daga majalisun hira, kafafen labaru zuwa cikin motocin haya duk batun ƙarancin Naira a ke yi kuma ba alamun samun sauƙi daga bayanan da a ke samu. Naira ba ta samuwa cikin sauƙi daga duk hanyoyin da a kan nema da su ka haɗa da na’urar ATM ta banki, masu POS da ma ‘yan canjin kuɗi.

Wannan dai kamar a tarihin canjin kuɗin Nijeriya ya zo da tangarɗa ainun don in kuɗi su ka shiga banki ba sa fitowa yanda ya dace. An wayi gari da matuƙar ƙarancin tsoffi da sabbin kuɗin. Lokacin da gwamnatin shugaba Buhari ta soja ta yi canjin kuɗi da a ka bayyana hikimar rutsawa da ‘yan almundahana ne ‘yan siyasar zamanin mulkin Shehu Shagari sai lamarin ya juye ya shafi ’yan kasuwa da kuma mazauna yankunan karkara inda wasu tun wancan karayar arziki da su ka samu ba su sake farfaɗowa ba.

Wasu ma an haƙiƙance haka su ka koma ga Allah cikin mawuyacin yanayi. A lokacin wasu sun taho wa imma a makare ko kuma sun ƙasa samun shiga banki don dogon layi ko ma wasu sun gamu da ‘yan damfara da su ka karɓe kuɗin da sunan za su canja mu su sai shiru ka ke ji wai Malam ya ci shirwa.

Yanzu kuma an samu cigaban zamani ta hanyar amfani da na’ura wajen tura kuɗi ba tare da riƙe takarda ba. Hakan ya kawo wani zaɓi ga wasu ajin mutane na iya taɓuka wasu lamura ta fuskar kuɗi amma wasu tarin mutane da ba su da ko asusun bankin balle su samu katin na’ura sun tashi a tutar ba hanyar zaɓin sauƙi.

Masu ƙananan sana’o’i da kan dogara ga takardun kuɗi duk sun karye kuma ko da masu samun kuɗin a wani lokaci daga masu POS sai sun biya caji mai tsadar gaske kafin su riƙe takardun kuɗin. Wato gaskiyar magana babban bankin Nijeriya CBN bai bayyanawa mutane ainihin yadda lamarin ya ke ba fiye da kawai su kai kuɗin su banki.

Kazalika har yanzu ba bayanin adadin sabbin kuɗin da a ka buga. Wannan tsari na yin dungu don cimma wata manufa ya jefa mutane a amincewa da duk wata jita-jita kan canjin. ’Yan siyasa su ka fara nuna don hana su lashe zaɓe ne, daga nan wasu masu sharhi su ka ce don tilastawa ne ko da wahala sai lalle darajar Naira ta farfaɗo.

Dalilan bankin dai har da ɓarayin daji ma za su daina satar mutane ko kuma ya zama wajibi su turo kuɗin da su ka ɓoye don canja sai a rutsa da kuɗin asusu ba tare da an sake kuɗin ba. Ko hakan ya yi tasiri ko bai yi ba akasarin mutanen kasa da dama ke cikin wahalar ƙuncin tattalin arziki sun ƙara shiga halin takaici ne kawai.

Har dai tsare-tsaren gwamnati na sauƙin rayuwa na da wani tasiri na zahiri da an gani a ƙasa. Ba wani mamaki ba da a kan samu wasu bankuna na ɓoye kuɗin sannan zai yiwu kuɗin na zurarewa su faɗa hannun ‘yan siyasar da ba a son su yi amfani da kuɗin wajen sayen ƙuri’a. Idan ma dai manufar gwamnatin na da kyau to shirin ya zo ma ta a makare ko ta fafa gora ranar tafiya kuma ba lalle ba ne ma sabuwar gwamnati in Allah ya sa an yi zaɓe lafiya ta cigaba da wasu manufofin.

Za ka ga manufar shirye-shirye daban waɗanda ta ke shafa daban. Wani abun da a kan yi tsammani a irin wannan lokaci shi ne jawabin shugaban ƙasa ga ’yan ƙasa idan an samu ƙalubale da ya shafi miliyoyin jama’a.

To babu jawabin sai dai abun da a ke gani na zahiri duk matakan da gwamnan babban bankin ke ɗauka da mara baya 100% na shugaba Buhari. Emefiele ya cancanci a yi wa ma sa kirari da GWAMNA KO GEZAU bisa ma’anar ba ya ko damuwa da ƙorafin da jama’a su ke yi ko umurnin da kotu ke bayarwa tun da a tarihin gwamnatin Nijeriya ba lalle ba ne ta mutunta hukuncin kotu kan abun da ya saɓa da muradun ta.

Zai iya zama abun lura yadda ta kai ga wasu gwamnoni da su ka haɗa da ‘yan gani kashenin shugaba Buhari kuma ’yan jam’iyyar gwamnati su ka ɗauki matakan shigar da gwamnatin ƙara kotu don tilasata babban bankin ya sauya matsaya. Idan wannan ya fito daga gwamnonin adawa ba za a yi mamaki ba.

Cikin gwamnonin ma har da wanda ya samu nasara a inuwar adawa amma ya yi wuf ya shige jam’iyyar gwamnati don amincewa da manufofin ta ko ganin hakan shi ne zavi mai kyau. Daga bisani sauran gwamnoni daga ƙungiyar gwamnonin sun ɗauki matsaya daya ta neman dakatar da tsayar da karvar tsoffin kuɗin. A baya dai in ka ga gwamnoni sun tsaya kai da fata kan abu to su kan yi nasara a saurare su amma wannan batu ya zama na daban.

Ba ma haka ba maimakon gwamnonin su samu yabo daga jama’a cewa sun dau matsayar ganawa da shugaba Buhari don sama mu su sauƙi, sai mutane da dama su ka yi ca akan gwamnonin sun a ma su cewa a ina gwamnonin su ke lokacin da a ka qara farashin mai? Me gwamnoni su ka yi kan kashe-kashen da ’yan bindiga ke yi?

Wace rawar taimako gwamnonin su ka taka lokacin cutar annoba da sauransu. Wannan yanayi ya wuce adawar mai kuɗi da talaka ko gwamnati da jama’ar ƙasa. Za a iya cewa ta inda matsalar ta shafi mutum, ta nan ne zai bayyana ra’ayin sa ko kukansa.

Ƙalubalen ya zama tamkar yunwa, fyaɗe yaro, fyaɗe babba. Ko me gwamnatin shugaba Buhari ke son cimmawa ne ko gadarwa sabuwar gwamnati da wannan tsari? ga dai tambaya da lokaci ne zai kawo amsar ta in da sauran shan ruwan mu za mu gani.

An ba da labarin cewa ƙasashen duniya kan canja kuɗi amma ba sa kafa wani wa’adi na daina aikin tsoffin kuɗi kuma su kan buga sabbin a wadace. Tsarin Nijeriya ya sha bamban da hatta Amurka da Nijeriyar ta dauko wannan tsari na shugaba mai cikekken iko daga gare ta.

Tsarin ya sha bamban da na Birtaniya da ta yi wa Nijeriya mulkin mallaka. Tsarin ya sha bamban da ƙasar Saudiyya da dubban ’yan Nijeriya Musulmi kan shiga ƙasar don ayyukan ibada.

Duk da ba lalle sai Nijeriya ta bi tsarin wata ƙasa ba, amma me ya sa ta bar ’yan lasa cikin wahala bayan ma ta yi alƙawarin inganta rayuwar jama’a ne? an zaɓi gwamnatin Buhari a 2015 don kawo sauƙi ga al’ummar ƙasa da yanzu za a ƙara wata tambayar shin an samu sauƙin da a ke buƙata?

Gwamnatin jihar Kano ta rufe babban shagon WELLCARE don yadda a ka same shi da babban abun takaicin kin karɓar tsoffin kuɗi.

Hukumar kula da ingancin kaya ta ɗauki matakin biyo bayan amincewa ko umurnin hakan daga gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje.

Gwamnatin Kano dai na kan gaba wajen nuna matuƙar damuwa ga yadda canja kuɗi ya kawo matsala ga talakawa don haka ma ta buƙaci mutane su cigaba da amfani da tsoffin kuɗin kafin samun wani hukunci kenan daga Kotun Ƙoli ko kuma matsaya daga babban banki.

Bayan ɗaukar matakin rufe shagon, masu mallakar shagon sun rubuta takardar neman ahuwa ga gwamnatin da roƙon a buɗe mu su shagon da ya ke nuna za su koma kenan karɓar tsoffin kuɗin daga hannun jama’a masu buƙatar kaya.

In za a tuna gwamnatin Kaduna, Kogi da Zamfara sun shigar ƙara Kotun Ƙoli don neman dakatar da daina karvar kuɗin daga 10 ga wata inda kotun ta amince da hakan kafin kammala sauraron ƙarar.

Godwin Emefiele ya yi kememe ya qi amincewa da umurnin Kotun Ƙoli na cigaba da amfani da tsoffin kuɗi har sai an kammala sauraron ƙarar da jihohi 3 su ka shigar.

A ziyarar da ya kai ma’aikatar lamuran ƙasashen waje, Emefiele ya ce ba wani dalilin ƙara wa’adin daga ranar 10 ga wata don an ɗauki matakan da su ka haɗa da iya karɓar kuɗi a kan kantar bankuna don sauƙaƙa wa mutane damar samun kuɗin.

Gwamnan ya ƙara da cewa za a cafke duk wani mai na’urar POS da ke cajin fiye da Naira 200 kan fitar da kuɗi matuƙar a ka kama shi da laifin.

Alamu na nuna babban bankin da ke da goyon bayan shugaba Buhari na neman biris da umurnin babban bankin tamkar ba a ba da wani umurni ba.

Alamu na nuna burin da a ke neman cimmawa kafin ganin sauƙi sai bayan kammala babban zaɓen nan na ranar 25 ga watan nan.

Kammalawa;

Masanin tsarin mulkin Nijeriya da wasu ƙasashen ƙetare Barista Mainasara Kogo Umar ya ce ya zama wajibi babban bankin Nijeriya ya bi umurnin babbar kotu bisa tanadin dokokin Nijeriya.

Da ya ke sharhi kan umurnin cigaba da amfani da tsoffin kudi da bankin ya ƙi sauraro, Mainasara ya ce raina umurnin kotun tamkar neman maida ƙasa ne wajen da ba doka kuma in an samu yanayin da ba a bin doka, ƙasa za ta iya shiga garari kowa ya riƙa yin abun da ya ga dama.

Lauyan ya ce, a duk lokacin da kotu ta yanke hukunci mai daɗi ne ko marar daɗi to ba makawa a yi biyaiya matuƙar a na son zaman lafiyan ƙasa.

Barista Umar ya ce duk ƙasar da ke watsi da kotuna, to ta kama hanyar rushewa ne.

In Allah ya yarda za a jira ranar 22 ga watan nan don dawowa Kotun Ƙoli a ga matakin da za ta ɗauka bayan ɗage sauraron ƙarar daga ranar 15 ga watan nan.