2023: Mun gamsu da manufofi biyar na Atiku, inji Uwani Hamsal

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe

Wata ‘yar siyasa a Jihar Gombe kuma jigo a tafiyar yaqin neman zaven ɗan takarar gwamnan jihar a Jam’iyyar PDP Muhammad Jibrin Barde, Hajiya Uwani Hamsal, ta ce ‘yan Nijeriya sun gamsu da ajandoji 5 da ɗan takarar shugabancin Nijeriya Atiku Abubakar, ya zayyana.

Hajiya Uwani Hamsal, ta ce ajandoji 5 da suka ƙunshi, inganta tsaro da farfaɗo da harkar noma, da ilimi da kasuwancin da kuma samar da ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya da ma su ne abinda suka daɗe suna ci wa ‘yan Nijeriya tuwo a ƙwarya.

Hajiya Uwani, ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ta kira a gidanta a Gombe inda ta ce ba shakka bayan waɗannan ajandojin Alhaji Atiku Abubakar, yana da kyakkyawan shiri ga ƙasar nan domin ya taɓa zama mataimakin shugaban ƙasa ya san matsalolin Nijeriya ciki da waje.

Ta ce ko rufe kan iyakokin Nijeriya da aka yi aka ƙuntata wa ‘yan ƙasa ya ce da zarar ya ci zaɓe zai buɗe su sannan kuma zai kawo ƙarshen matsalar ƙarancin abinci.

Uwani Hamsal, ta ƙara da cewa kar ‘yan Nijeriya su raba ɗayan biyu yadda ta san Atiku, sai ma ya hau kujerar shugabancin ƙasa za a gane ashe da tun farko ma shi aka zaɓa a 2019 da yanzu wannan ƙuncin rayuwar ba ma cikinta.

“Matsalar canjin kuɗin nan ba shi ne ‘yan Nijeriya ke buƙata ci gaba da walwala suke nema amma sai ga shi Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC ya nunawa duniya cewa jam’iyyar su ba jam’iyyar da za a sake zava ba ce,” inji ta.

“‘Yan Nijeriya ku zaɓi Jam’iyyar PDP mai alamar lema a lokacin zaɓe don kar ku bari a sake jefa ƙasar cikin ruɗani maimakon a ceto ta,” ta kara faɗa.

A jihar Gombe kuma ta yi amfani da wannan damar ta kira yi al’ummar jihar da cewa a ranar zaɓen gwamna su zaɓi Muhammad Jibrin Barde na Jam’iyyar PDP domin shi ne zai ceto jihar daga halin da ta shiga a hannun ‘yan koyo.

Daga nan Uwani Hamsal, ta gargaɗi, jama’a da cewa su zaɓi Jam’iyyar PDP daga sama har ƙasa kar su bari a rasa wata kujera domin idan Atiku da Ɗan Barde suka ci zaɓe muddin ba su da mataimaka ba za su ji daɗin gudanar da mulkin ba, don haka ta ce a zabi PDP sak.