Idan na ci zaɓe zan kammala aikin haƙar man Kolmani —Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗan takaran Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, ya ce idan ya ci zave zai tabbatar aikin haƙo man fetur na garin Kolmani da ke Jihar Gombe bai tsaya ba.

Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin yaƙin neman zaɓensa a Jihar Gombe, inda ya ce muddin aka zaɓe shi gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen kammala aikin.

“Zan tabbatar gwamnatina ta ɗora kyawawan ayyuka daga inda Shugaba Muhammad Buhari ya tsaya,” inji Tinubu.

Tinubu, ya kuma yaba wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, na gina gandun masana’antu a garin Daɗin Kowa a jihar, wanda zai samar wa ɗinbin al’umma aikin yi.

A nasa jawabin a filin taron, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, cewa ya yi APC jam’iyya ce da ta ƙuduri aniyar ci gaba da ɗorawa kan ayyukan raya ƙasa da ta ke gudanarwa don ci gaban jihar da ma Nijeriya baki ɗaya.

“Zaɓen Tinubu da Shettima, zaɓe ne na ci gaban Nijeriya, hakan zai taimaka na ƙara samar da wasu ayyukan raya ƙasa,” a cewar gwamnan.

Tinubu na ci gaba da shan alwashin kammala ayyukan da gwamnatin Shugaba Buhari za ta bari ba ta kammala ba.