Na cika alƙawuran da na ɗauka wa ‘yan Nijeriya – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa alƙawuran yaƙin neman zaɓen 2015 da ya yi wa ‘yan Nijeriya gwamnatinsa ta cika.

Shugaban ya bayyana haka ne a wajen bikin yaye ɗaliban Jami’ar Tarayya karo na 7 da aka yi a garin Oye-Ekiti na Jihar Ekiti, inda ya bayyana cewa ya bayar da gudunmawa ta fuskar tattalin arziki, tsaro, da yaƙi da cin hanci da rashawa.

Ya ƙara da cewa Shugaban Ƙungiyar Benchers ta Nijeriya Cif Wole Olanipekun (SAN) da tsohon manajan darakta na bankin First Bank Bisi Onasanya da kuma tsohon kyaftin ɗin Super Eagles Segun Odegbami, an ba su lambar yabo saboda gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban ƙasa.

Ya ce alƙawuran da ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓe sun ta’allaƙa ne kan inganta tattalin arziki, inganta tsaro, da yaƙi da cin hanci da rashawa, ya kuma nuna jin daɗinsa da yadda waɗannan ɓangarori uku suka samu ci gaba sosai.

Da yake nasa jawabin, Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta ɗora Nijeriya a kan turbar da ba za a iya dawowa da ita ba, duk da cewa har yanzu ƙasar ba ta kai matsayin yadda ya kamata ba ta fuskar samar da ababen more rayuwa.

Ya ce, “Bari in tunatar da kowa cewa tushen yaƙin neman zaɓena na zama Shugaban Ƙasa a 2015 shi ne alƙawarin inganta tsaro, ƙarfafa tattalin arziki, da yaƙi da cin hanci da rashawa. Godiya mai yawa ga Allah Maɗaukakin Sarki, na samu ƙarfin gwiwa wajen tabbatar da cewa mun cika alƙawuran nan guda uku.

“A lokacin da aka rantsar da ni, al’ummar ƙasar na fama da ta’addanci da sauran matsalolin rashin tsaro. Ina mai tabbatar da cewa an yi yaƙi da ta’addanci kuma an yi nasara, domin an ƙwato duk yankunan da mahara suka kafa tutarsu. Kuma a halin yanzu ta’addanci a Nijeriya ya ƙare.

“Har ila yau, abin lura ne cewa a ƙarƙashin jagorancina, Nijeriya ta tashi daga taɓarɓarewar da durƙushewar tattalin arziki ta zama ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziki a nahiyar. Wannan ba aiki ba ne mai sauƙi. Yana iya zama kawai sakamakon ingantaccen dabarun gudanar da mulki.

“Kafin a zaɓe ni a matsayin Shugaban Ƙasa a 2015, ƙasar ma ta fuskanci cin hanci da rashawa. Haka kuma ana jin cewa ayyukan da gwamnatina ta yi da suka haɗa da aiwatar da tsarin TSA, manufar bayar da bayanan sirri, da kuma ƙara ƙaimi wajen gurfanar da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa, sun taimaka wajen daƙile ƙaruwar cin hanci da rashawa a ƙasar.

“Bugu da ƙari kan muhimman abubuwa guda uku, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta sake gyara fannin ilimi ta hanyar ƙara yawan kuɗaɗen da ake kashewa wajen samar da jarin ɗan Adam da samar da ababen more rayuwa.

“Duk da cewa ba zai yuwu a ware dukkan kuɗaɗen da ƙasar nan ke da su a fannin ilimi ba, amma sanin kowa ne cewa gwamnatina tun lokacin da aka kafa ta a ranar 29 ga watan Mayun 2015, ta ci gaba da qara yawan kuɗaɗen da ake ba fannin a kasafin kuɗinta na shekara.”

Shi ma da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Abayomi Fasina, ya bayyana cewa cibiyar ta zana wa kanta wani katafaren tsarin ilimi na ƙasa da ƙasa a cikin lokaci mai tsawo.

Fasina ya taya ɗaliban da aka yaye murnar samun nasarar karatunsu, sannan Fasina ya buƙace su da su ci gaba da zama wakilai nagari a jami’ar da kuma kyautata sunanta.