Yadda mai juna-biyu ta rasu a asibitin Nasarawa…saboda ƙin karɓar tsohon kuɗi a Kano

*Mijinta ya zayyana yadda lamarin ya faru
*Mun fara bincike kan lamarin, inji hukumar asibitocin jihar
*Gwamnatin Tarayya ce ta saka ’yan Nijeriya a cikin matsalar – Gwamnatin Kano

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Wata mai juna-biyu, Malama Shemau Sani Labaran, ta rasa ranta a lokacin da ta ke naquda sakamakon ƙin karɓar tsofaffin takardun kuɗi da asibitin Nasarawa dake Jihar Kano ke yi, kamar yadda mijinta, Bello A. Baffancy, ya tabbatarwa da Blueprint Manhaja.

Idan dai za a iya tunawa, harkokin rayuwa su na samun cikas a Nijeriya sakamakon canjin fasalin Naira 200, 500 da 1,000 da Babban Bankin Nijeriya ya yi, inda qarancin kuɗi ya jefa mutane a cikin mawuyacin hali.

A tattaunarawasa da mu Baffancy ya zayyana mana yadda lamarin ya faru har ya kai ga rasa ran maiɗakin tasa, yana mai cewa, “Matata sunanta Shemau Sani Labaran, kuma abinda ya faru a wannan rana shine, mun je asibitin Muhammad Abdullahi Wase, wato asibitin Nasarawa.

Matsala ta farko da muka fara fuskanta ita ce, wannan asibitin ba sa karvar tsohon kuɗi, sai sabon kuɗi, waɗannan masu bular nan, sannan kuma ba su da POS. kuma ba POS wanda za ka cire kuɗi ka ba su. Abinda suke amfani da shi, akwai wani Polaris Bank, shi za su ba ka, za ka yi taransifa.

Taransifar nan kuma idan ka yi ta, ba za a ba ka rasit ba na cewar ka biya a ba ka magani ko a duba maras lafiyarka ba, sai sun ga ‘alert’ ɗin ya faɗo musu. Duba kuma halin da ake ciki yanzu ‘alert’ ɗin ba ya zuwa da wuri, a wannan lokacin maras lafiya ɗauki ya ke so.

“Bayan duk waɗannan hanyoyi da muka bi, ba POS, ‘alert’ ɗin kuma ya gama jinkirin da zai yi ya sauka, aka ba mu resit muka je inda wajen bada magani ya ke muka bayar, aka ba mu magunguna, mu na dawowa mun buɗe fayil, mun yi komai, sai kuma aka ce mana babu gadon da za a ɗora ta.

“Ƙarshe wani ma’aikaci ya ce, akwai gado, amma gadon tsirararsa ne, waya ce, babu katifa. Matata da kanta ta ce ta aminta, don ita ta san halin da ta ke ciki, za a shimfiɗa zannuwa a ɗora ta, ta amince da haka.

“Ana ƙoƙarin haka ne muka samu wata baiwar Allah ta yi mana hanya sakamakon wata ‘-n-charge’ ta wannan asibitin da aka kirawo a waya ta gaya mata matsalarta. Tana kiran su ta ce a ba su waya. Ana ba su waya, sai ga shi an je an ɗauko mana gado mai kyau da katifa. Aka zo aka kwantar da matata.

“To, wannan jinkiri da aka yi ya taimaka wajen matata ta riqa zubar da jini, ta riqa zubar da jini! Matata ta zubar da jini ya fi cikin bokitin fenti. Ɗan farin ‘plastic’ ɗin nan, wanda a ƙarshe aka ce ai yaron da ya ke cikinta ma ya mutu, sai an sa mata ruwan naƙuda.

“Aka sa mata ruwan naƙuda ta haife shi a matsayin matacce. Jariri yana gefe a na ƙoƙarin za a ceto rayuwarta, ita ma jinin nan da ya tsinko suka yi rubuce-rubucen allurorinsu da magungunansu, aka je a gurguje-a gurguje aka je aka ƙara yin wannan tiransida ɗin nan dai, aka jira aka ga ‘alert’, muka karɓi resit muka je ɗakin karɓar magani aka ba mu allurori aka zo aka ɗaura mata.

“Bugu da ƙari, aka nemi jini leda uku, muka nemo waɗanda za su bada jini, aka zo, domin sun ce sabon jini suke so. Na kirawo cikin mutanena aka zo aka ɗauki jini, aka zo a ka ba su. Jinin ma dai guda ɗaya suka yi mata amfani da shi.

“To, cikin wannan galabaita… Ta riga ta galabaita, Allah cikin ikonSa ita ma wajen ƙarfen ukun dare ta ce, ga garinku nan. Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Haka da asubar nan aka ban gawar matata da gawar jaririyata!

“Wannan sakacin da ya fara bada gudunmawa shine, rashin karɓar tsohon kuɗi, domin idan da an karɓi tsohon kuɗi, wa’adin matata na san ya yi, amma dai da abin ba zan ɗora shi akan wannan ba!

“Ba a karɓar tsohon kuɗi, sannan ba POS, tiransifa kuma idan ka yi ba za a yarda ka yi ba, ko da a idonsu ka yi, sai an ga ‘alert’”

Daga nan sai ya tabbatar zargi kan hukumomin asibitin da karvar cajin kuɗi, kamar yadda masu POS ke yi, duk da cewa, tiransifa ake yi musu.

“Ƙwarai da gaske! Ni ba labari aka ban ba. duk tiransifar da na yi, wallahi azim sai da na sa caji. Akwai wanda na sa cajin ɗari-ɗari, akwai wanda na sa na ɗari bibbiyu. Ni na sa cajis.”

A yayin da Blueprint Manhaja ta tuntuɓi Shugabar Asibitin ta Nasarawa, Dr. Rahila Garba, ta ce, haɗa mu da Jami’in Yaɗa Labarai na Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano, Malam Ibrahim Abdullahi, wanda ya bayyana cewa, dukkan waɗannan zarge-zarge a yanzu ne hukumomi ke samun bayanai kansu, kuma a yanzu haka an samo fayil ɗin Marigayiya Shemau, don bin diddigin yadda lamarin ya faru da kuma ɗaukar matakan da suka dace.

Daga nan sai ya yi alƙawarin yi wa manema labarai da iyalan marigayiyar cikakken bayani kan lamarin.

Idan za a iya tunawa, Gwamnatin Jihar Kano ta haramta wa guraren harkokin kasuwanci ƙin karɓar tsofaffin takardun kuɗin, saboda maganar tana gaban kotu har ma Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abudllahi Umar Ganduje, ya rufe wasu gurare.

Wannan ya sanya Blueprint Manhaja ta tuntuɓi Shugaban Kwamitin Ko-ta-kwana na Jihar Kano kan lamarin, Dr. Baffa Babba Dan Agundi, wanda ya shaida mana cewa, Gwamnatin Jihar Kano ta na yin bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta shawo kan matsalar, amma ya ƙara da cewa, duk da ya ke Gwamnatin Tarayya gwamnatin jam’iyyarsu ce ta APC, amma hakan ba zai hana su ɗora alhakin duk waɗannan matsaloli da ’yan Nijeriya ke fuskanta kanta ba, saboda ƙin biyayya da umarnin Kotun Ƙoli, wacce ta dakatar da gwamnati daga haramta amfani da takardun kuɗin.

Ya ce, su kansu ’yan kasuwar da suke ƙin karɓar kuɗin ba laifinsu ba ne, domin Babban Bankin Nijeriya (CBN) ne ya ke zare musu idanu kan amsar takardun kuɗin. Amma ya ƙara da cewa, gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje za ta yi iyaka ƙoƙarinta wajen ganin ta ƙwato haƙƙin al’ummarta da walwalar jama’arta.