Lalata takardun Naira 200: Emefiele ya gana da shugabannin bankuna

Daga AMINA YUSUF ALI

A yayin da ake tsaka da yaɗa rahotanni game da cewa, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya lalata  takardun tsofaffin kuɗi na Naira 200, Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya je don ganawa da shugabannin zartarwa na bankunan Nijeriya. 

Idan za a iya tunawa, Shugaban Ƙasa  Muhammadu Buhari ya yi jawabin da ya sanar da ‘yan Nijeriya cewa, ya bayar da damar a cigaba da amfani da tsofaffin takardun Naira 200 har zuwa nan da kwanaki 60.

Buhari ya bayyana cewa, ya bayar da wannan umarnin ne, saboda sauƙaƙa wa mutane wahala, wanda shi ya sa ya ba wa Bankin CBN umarni a kan su saki tsofaffin takardun Naira 200 su cigaba da zazzagawa tare da sababbin takardun Naira 1000, 200 da 500 har zuwa lokacin da wa’adinta zai qare a ranar 10 ga Afrilu, 2023.

Kodayake, akwai kuma rahotanni a kan cewa, dukkan tsofaffin kuɗaɗen da aka kai bankuna an lalata su.

Sai dai kuma Emefiele, bayan ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ya bayar da tabbacin cewa, za a samar da takardar Naira 200 tsofaffi su wadata ba tare da ɓata lokaci ba. 

Kuma ya roƙi ‘yan Nijeriya a kan su yi haƙuri su tafi tare da sabon tsari domin zai taimaka wa tattalin arzikin ƙasa.  

Haka zalika nan, Gwamnan CBN ya bayyana cewa, bankin zai yi duk mai yiwuwa, saboda ya sauƙaƙa wa ‘yan Nijeriya wahalhalun da suka shiga sakamakon rashin kuɗi a hannu.