Tattalin arziki da batun sake fasalin Naira

Manhaja logo

Rashin aiwatar da manufofin sake fasalin Naira ya yi tasiri sosai ga tattalin arziki da jama’a. A saboda haka qarancin takardun kuɗin na naira ya ƙara taɓarɓara rayuwar ’yan Nijeriya. Har ila yau, matsalar man fetur ma na ƙara dagula al’amura a ƙasar.

Bayan wannan kuma, ’yan Nijeriya na kokawa da matsalar wutar lantarki da hauhawar farashin kayayyaki. Hakan dai na zuwa ne duk da jinkirin da Kotun Ƙoli ta yi biyo bayan umarnin wucin gadi da ta bayar na hana babban bankin ƙasar CBN ci gaba da aiwatar da wa’adin da ya ɗiba a ranar 10 ga watan Fabrairu na wa’adin daina karɓar tsofaffin takardun kuɗi.

Ko da yake babban bankin na CBN ya ce tsarinsa na canja kuɗi ba wai an tsara shi ne don wahalar da ’yan Nijeriya wajen samun sabbin takardun kuɗi ba, sai dai don ƙarfafa hada-hadar kuɗi. Zanga-zangar da aka yi a wasu manyan jihohin ƙasar nan sakamakon matsalar kuɗi ta sa wasu bankunan rufe wasu rassansu.

Har ila yau, har yanzu ana ganin al’amuran sun ƙazanta a wasu manyan na’urori fitar da kuɗi na ATM yayin da dubban mutane ke fafutukar samun sabbin takardun naira.

Ƙananan ’yan kasuwa da matsakaita da manyan ’yan kasuwa na jin raɗaɗin ƙaranci sabbin takardun kuɗi da kuma tsadar man fetur. Taɓarɓarewar manufofin sake fasalin naira zai gurgunta harkar kasuwanci da noma.

Har ila yau, zai yi tasiri ga sauran sassa masu muhimmanci na tattalin arziki, musamman sarkar darajar masana’antu da kuma ɓangaren ayyuka.

Sakamakon ƙarancin sabbin takardun kuɗi na Naira, an samu cikas sosai a kasuwar hada-hadar kuɗi sakamakon matsalar musayar kuɗaɗe. Ɓangaren kasuwanci, alal misali, yana ba da gudummawar kusan kashi 14 cikin 100 na tattalin arzikin ƙasar, wanda darajarsa ta kai Naira tiriliyan 35. Ɓangaren noma, wanda ke ba da gudummawar kusan kashi 25 cikin 100 ga tattalin arzikin ƙasa an kiyasta kimanin Naira tiriliyan 62.

Yawancin ayyukan da ake yi a waɗannan sassa na ko dai a yankunan karkara ne ko kuma a fannin tattalin arziki na yau da kullum. Waɗannan su ne sassan da suka sa tattalin arzikin ya tsaya ƙam ta fuskar haɓaka ƙasa tun bayan ɓullar cutar Korona a shekarar 2020.

Bisa ƙididdigar da Ƙungiyar ’Yan Kasuwa, Masana’antu, Ma’adinai da Noma ta Nijeriya (NACCIMA) ta nuna, ɓangaren ya samu raguwar tallace-tallace kusan kashi 20 cikin 100 na kayayyakin masarufi da kuma kashi 30 cikin 100 na masana’antun tun lokacin da aka fara ƙaranci sabon kuɗin Naira da ƙarancin man fetur.

Waɗannan sassa ne waɗanda ke ba da gudummawar mafi yawan tattalin arziki. Ƙarancin albarkatun man fetur ya haifar da cikas ga ‘yan kasuwa da ɗaiɗaikun mutane. Har ila yau, ya yi mummunan tasiri a kan zuba jari. An yi kiyasin cewa rikicin na iya jefa kuɗin Nijeriya Naira tiriliyan 100 na tattalin arziki cikin haɗari.

Maganar gaskiya ita ce, kasuwar samar da kayayyaki a cikin ƙasa zai lalace. Hakan zai faru ne saboda abin da masana’antun ke samarwa ba za a sayar da shi ba saboda ana fama da ƙarancin kuɗin da ke zagayawa da amfanin gona. Al’amarin zai munana.

Yayin da ƙasa da mako biyu ya rage a gudanar da zaɓukan 2023, ƙarancin kuɗin da ake samu na Naira na ƙara matsa lamba ga gwamnati. Muna ba da shawarar cewa a samar da matakan gaggawa don magance rikicin da ke ƙara ruruwa. Ba tare da samar da sabbin takardun kuɗi na Naira ba, mai yiyuwa ne ƙasar ta faɗa cikin wani rikici mara misaltuwa wanda zai iya rikiɗewa zuwa wani abu.

Muna kira ga ’yan siyasa da su kasance masu kishin ƙasa, su sanya ƙasar ta zama mafi fifiko. Lokaci ya yi da ya kamata ’yan siyasa su ajiye duk wani abu, su saka manufar gyara ƙasa a gaba. Manufar sake fasalin naira yana da kyau amma lokacin da aka aiwatar da shi ne ya zama ba daidai ba.

Gaba ɗaya, ana buƙatar tsarin ɓangaranci cikin gaggawa don magance matsalolin da ke tattare da manufofin sake fasalin naira. Ya kamata gwamnati ta bi shawarwarin Majalisar Dokoki wajen magance matsalar ƙarancin Naira.

Mun amince da shawarwarin da Majalisar ta bayar, inda ta buƙaci CBN da ya yi la’akari da sake yin amfani da tsofaffin takardun kuɗi na Naira domin rage zaman ɗar-ɗar a faɗin ƙasar nan ko kuma a samar da sabbin da za su wadashi ko ina.

Hakan dai ya yi daidai da shawarar da Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) suka bayar, inda a makon da ya gabata suka buƙaci CBN da ya ƙara wa’adin daina karvar tsoffin kuɗi.

A yayin da Kotun Ƙoli ta yanke hukunci kan batun shigar da ƙarar da gwamnatin jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara ta gabatar a gabanta, ’yan Nojeriya na son ganin an kawo ƙarshen wannan lamari domin kada ya dakatar da zaɓe mai zuwa. Dole ne dukkan hannaye su kasance a wuri ɗaya don tabbatar da cewa zaɓen ya kasance cikin gaskiya da sahihanci.