Bayan wata 11, an sako ma’aikacin lafiyar da aka yi garkuwa da shi a Borno

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Maiduguri

‘Yan bindiga sun sako ma’aikacin kiwon lafiya, Bulama Gaidam, wanda suka yi garkuwa da shi kimanin watanni 11 da suka gabata a Jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan T’ta’addan sun saki Bulama ne a garin Gubio kana daga bisani aka wuce da shi zuwa Maiduguri domin miƙa shi ga iyalansa.

Sai dai rahotannin ba su bayar da cikakken bayani ba kan ko an biya kuɗin fansa kafin a sako shi, ko ba a biya ba.

An yi garkuwa da Bulama ne tun a cikin watan Maris na 2022, a lokacin da mayaƙan ISWAP suka kai wani farmaki Ƙaramar Hukumar Gubio, mai tazarar kilomita 70 daga Maiduguri, babban birni Jihar Borno.

A lokacin mayaƙan sun bayyana cewa sun kai wannan farmaki ne domin su kwashi kayan abinci da man fetur daga wata motar ƙungiyar ayyukan jinƙai a yankin.

Farmakin da ya tilasta wa mazauna garin arcewa daga garin domin neman tsira da rayukansu, wanda bayan fitar ‘yan ta’addan jama’a suka koma gidajensu.