Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Kwamitin Shugaban ƙasa kan Sauya Tsarin Haraji da Manufofin Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa kuɗaɗen shiga daga kadarorin intanet kamar cryptocurrency ba sabbin abubuwan haraji ba ne a tsarin Nijeriya, domin tuni dokar harajin mutum ta tanade su tun da farko.
Ya ce, sabon tsarin dokar haraji da aka amince da shi bai ƙirƙiri sabbin haraji ba, sai dai ya bayyana, ya sauƙaƙa, kuma ya daidaita tsarin da ke akwai.
Oyedele ya yi wannan bayani ne a taron tattaunawa da manema labarai da masu tasiri da masana da aka gudanar a Lagas a ƙarshen mako, inda ya yi ƙoƙarin fayyace abin da sabon tsarin haraji yake nufi.
“Ba a ƙara wa mutane haraji ba. Duk wanda yake samun kuɗi ta hanyar sadarwa, yin tasiri a intanet, ko ta kadarorin dijital kamar cryptocurrency, ya riga ya kasance ƙarƙashin doka tun da farko,” inji shi.
“Sabbin dokokin kawai sun fayyace yadda ake aiwatar da wannan, tare da tabbatar da adalci — ciki har da ba da damar a cire asarar kuɗi idan ta taso.”
Ya ƙara da cewa, kyauta ko kuɗin da aka bayar ba tare da wata mu’amala ta kasuwanci ko sabis ba ba su cikin abin da ake harajewa.
Oyedele ya bayyana cewa babban burin wannan sauyi shi ne sauƙaƙa tsarin haraji na Nijeriya wanda ake ganin ya yi ƙalubale sosai.
“A halin yanzu, muna rage haraji da kuɗaɗen da suka haura 60 zuwa ƙasa da goma.
Manufarmu ita ce sauƙaƙa bin doka, kawar da haraji sau da yawa, da samar da tsari mai sauƙin fahimta da tabbas,” inji shi.
Ya kuma ƙara da cewa, sabbin dokokin ba don ƙara haraji aka tsara su ba, amma don tabbatar da adalci da bunƙasa tattalin arziki.
A cewarsa, da dama daga cikin harajojin da gwamnatocin baya suka kafa an soke su ko an dakatar da su, ciki har da: Harajin kashi 5 kan katin waya data, Harajin tsaro ta yanar gizo kan canjin kuɗi a banki, Harajin carbon kan robobin da ake amfani da su sau ɗaya, da kuma harajin mota da aka taɓa sanyawa.
