Sabuwar ƙungiyar ta’addanci ta yi iƙirarin hannu a kisan kiyashin Ngoshe, ta yi barazanar hari a Abuja da Maiduguri

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata ƙungiyar ‘yan bindiga ta yi ikirarin ita ke da alhakin ƙaddamar da mummunan harin da ya auku a ƙauyen Ngoshe da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno, inda sojoji da fararen da dama suka rasu tare da yin awon-gaba da mutane sama da 300 a harin na ranar Laraba.

Maharan sun yi wannan ikirari me a wani faifan bidiyo da jaridar NewsPointNigeria ta samo, inda aka ga mutane biyar suna bayanin yadda aka ƙaddamar da harin da kuma shelanta nufinsu na karɓe iko da yankin.

Da fari, an ruwaito cewa maharan sun farmaki ƙauyen ‘yan ta’addar sun kutsa cikin ƙauyen ne acikin dare, idna suka ƙaddamar da harin a wani sansanin sojoji da yankunan fararen hula.

Shaidu sun tabbatar da cewa, maharan sun cinna wuta a sansanin sojojin, sannan suka riƙe harbe-harbe da kuma ƙone gidaje da shaguna a ƙauyen.

Wannan al’amari ya jefa jama’ar yankin cikin firgici, inda da dama suka tsere zuwa ƙauyukan da ke kusa da su domin tsira da rayukansu.

A faifan bidiyon, an ga yadda ɗaya daga cikin su da ya yi bayani da harshen Hausa ya ce sun karɓe iko da Ngoshe da kuma shirya tarewa a can, yana mai cewa za su yi bikin sallah ƙarama a babban masallacin garin bayan Ramadana.

By Babaji