Sai an fifita harkar tsaro sannan Nijeriya za ta inganta – Shugaban NRI

Daga JABIRU A. HASSAN a Dutse

Shugaban Ƙungiyar Farfaɗo da Martabar Arewa da Kyautata Haɗin Kan Ƙasa ta “Northern Reformation and National Unity Initiative” (NRI), Alhaji Abubakar Adamu Haɗejia ya buƙaci ɗaukacin al’ummar Nijeriya da su bai wa sababbin hafsoshin tsaro cikakken haɗin kai da goyon baya, ta yadda za su cimma dukkanin nasarorin da ake buƙata domin kyautata zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan ƙasa.

Abubakar Haɗeja, ya yi wannan kira ne a ganawar su da wakilin mu a birnin Dutse, inda kuma ya sanar da cewa idan ’yan Nijeriya suka bada goyon baya da haɗin kai ta fuskar tsaro, ko shakka babu za a sami nasarar kawar da dukkanin wani abu da ke zama barazana ta fannin tsaro a ƙasa tare da bunƙasa zamantakewa a birane da karkara.

“Tsaro yana buƙatar a haɗa hannu ne tsakanin jami’an tsaro da al’umma domin zaƙulo waɗanda suke da hannu wajen aikata laifuka, sannan su kan su jami’an tsaro za su samu karsashi wajen kawar da ɓatagari daga cikin al’umma, musamman a wannan lokaci da ake buƙatar ganin komai yana tafiya cikin kwanciya hankali,” inji shi.

Shugaban ƙungiyar ta NRI ya kuma nunar da cewa suna aiki kowane lokaci domin tabbatar da ganin ana samun haɗin kai da ƙaunar juna tsakanin kowane vangare na wannan ƙasa kamar yadda shugabanni suke ta ƙoƙarin ingantawa, kuma a daidai wannan lokaci da Nijeriya ke buƙatar ci gaba da kasancewa cikin zaman tare ta kowane fanni.

A ƙarshe shugaban ya yi fatan cewa waɗannan sabbin hafsoshin tsaro za su sami ƙarin goyon baya da haɗin kai daga al’ummar ƙasar nan ta yadda kwalliya za ta biya kuɗin sabulu ta fuskar tsaro da bunƙasa zaman rayuwa kamar yadda lamarin yake a zamanin baya, tare da jaddada cewa Najeriya za ta fi dacewa  bisa zaman tare da taimakon juna maimakon iza wutar rikicin ƙabilanci ko addini da kuma ɓangaranci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *