Sai kun zama masu bin doka za ku iya kama masu karya doka, kiran IGP ga ‘yan sanda

Daga BASHIR ISAH

Muƙaddashin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, IGP Olukayode Egbetokun, ya umarci tawagar motocin ‘yan sanda da su daina saɓa dokokin amfani da hanya.

IGP ya ba da wannan umarni ne yayin ganawar da ya yi da tawagar ‘yan sandan kwantar da tarzoma da kwamndojin ‘yan sanda ranar Litinin a Babban Ofishin Rundunar ‘Yan Sanda da ke Abuja.

Egbetokun ya jaddada wa jami’an kan su sani cewa, tabbatar da bin doka da oda, kare rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne babban aikinsu.

Ya ƙara da cewa wajibi ne ‘yan sanda su yi aiki daidai da dokokin aikin ɗan sanda kuma a cikin yanayin da zai sa al’umma su martaba su.

Ya ce, “….bari in tunatar da ku cewar dole ne masu tabbatar da zaman lafiya su kasance tushen zaman lafiya.

“Wajibi ne waɗanda aikinsu ya danganci tabbatar da bin doka, su ma su zama masu martaba dokar ƙasa.

“Ba tare da bin doka ba, ‘yan sanda ba su iya kamawa da kuma hukunta masu karya doka ba,” in ji shi.