Sai yaro ya kai shekaru 12 zai shiga sakandare a sabon tsarin ilimi – Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ma’aikatar Ilimi ƙarƙashin jagorancin Minista, Tunji Alausa ta sanar da sabuwar doka dake nuna cewa sai ɗalibi ya kai shekaru 12 sannan za a ba shi damar fara karatu a makarantar sakandare bayan karatun firamare.

Rahotanni sun bayyana cewa an sanar da sabon tsarin ne a wani saƙon tsare-tsare ga makarantun kuɗi, wanda ma’aikatar ta fitar a kwanan nan da nufin inganta tsarin ilimin yara a makarantun.

A cewar saƙon, an tsara ilimin matakin farko a Nijeriya cikin shekaru tara inda za a yi shida a firamare, sai kuma uku a ƙaramar sakandare.

A yayin aiki da tsarin, za a sanya yaro a aji ɗaya na firamare a lokacin da ya/ta kai shekaru shida da haihuwa.

Ana ganin sabon tsarin a matsayin wanda zai bai wa ɗalibai damar kai wa shekaru 18 a yayin da suka kammala sakandare, wanda kuma shi ne wanda dokar ƙasa ta amince da shi don neman karatu a makarantun gaba da sakandare a gare su.

By Babaji