Sakacin jami’an tsaro na da nasaba da garkuwa da ƴan makarantar Maga, inji Gwamnan Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi Malam Nasir Idris ya ce awon-gaba da ɗaliban makarantar sakandaren mata ta Maga a jihar, yana da nasaba da sakacin jami’an tsaro bayan samun bayanin cewa akwai yiyuwar a kai farmaki a makarantar.

Rahoton wata jaridar yanar gizo ta ‘Pointblanknews’ ta wallafa cewa gwamna Malam Nasir Idris bayan ya isa makarantar da yammacin ranar litinin, inda ya bayyana cewa akwai jami’an tsaro da ke yi wa gwamnatinsa zagon-ƙasa duk da irin ƙoƙarin da yake yi kan harkar tsaro.

Ya ƙara da cewa bayan samun bayanan sirri daga hukumar jami’an tsaro na farin kaya (DSS) da kuma shawarwari an gudanar da taron gaggawa tare da ɗaukar matakin bai wa makarantar kariya wanda tuni aka yi amma sai gashi saboda sakacin jami’an tsaro da aka danƙa wa alhaki sun yi son rai, lamarin da ya janyo kai farmakin tare da kashe mataimakin shugaban makarantar da kuma yin awon gaba da dalibai ashirin da biyar (25) sai dai uku daga cikin su sun tsere

Gwamnan ya bayyana cewa ya ɗauki bayanin da jami’an tsaro na DSS da muhimmanci a ka haka ne saboda irin wannan ne ya faru a jihar Katsina a watan Disambar shekarar 2020 inda aka ɗauke sama da daliban firamare 300 a garin Ƙanƙara.

Ya ce, an kai jami’an tsaro ne da makamai ba don komai ba sai dai don su kare lafiyar daliban amma a maimakon haka kawai sai suka cigaba da ɗaukar hotuna tare da ɗaliban suka tafi da su sannan suka bar makarantar bayan mintuna talatin sai ga maharan.

Tuni gwaman da sauran shugabannin hukumomin tsaro da suka dafa masa baya sun kafa wani kwamiti don gano bakin zaren dalilin sakacin afkuwar wannan lamarin duk da bayanan sirri da aka samu da kuma ɗaukar mataki da aka yi.

Wani Malami da ya tsallake rijiya ta baya ya bayyana cewa ranar Lahadi jami’an tsaro sun daɗe cikin harabar makarantar tare da ɗaliban har na wani lokaci mai tsawo amma abin mamaki duk bai fi suna ficewa daga makarantar bai fi minti talatin ba sai aka kawo harin.

Gwamna Malam Nasir Idris ya yi amfani da ƙwarewar shugaban hukumar jami’an tsaro na farin kaya DSS inda ya umarce shi da ya jagoranci kwamitin don ganin an samu nasarar ceto waɗannan ɗaliban, da ya ke bayanai da ake samu dai sun tabbatar da ba a kashe yaran ba suna nan raye wanda in Sha Allahu ana sa ran dawowarsu cikin ƙoshin lafiya.

By Babaji