Sakamakon mai taimakon mabuƙaci tun a duniya yake zuwa – Maimuna Yusuf

“Ba na buƙatar kafa gidauniya kafin na tallafa wa mabuƙata”

Daga AMINU ALHUSSAINI AMANAWA

Samun ɗai-ɗaikun matan da kan fito suna taimaka wa al’umma na ƙashin kai, musamman ma taimakon marayu kusan lamari ne da ba a cika samu sosai ba a wannan zamanin. To amma sai dai a iya cewa lamarin ya soma canza salo, bayan da aka soma samun ɗai-ɗaikun matan da kan tallafa wa marayu na ƙashin kai ba tare da kafa ƙungiya ko gidauniya ba, a cewar su, suna yi ne saboda Allah, domin samun kyakkyawan sakamako daga wajen ubangiji. A zantawar da wakilinmu a Sakkwato ya yi da Hajiya Maimuna Yusuf, ɗaya daga cikin matan da ke tallafa wa marayu na ƙashin kai, ta bayyana dalillan da ya sanyata fito wa da shirin tallafa wa marayu da marasa ƙarfi, inda ma har ta ware ranar 11 ga watan Maris ɗin kowacce shekara a matsayin ranar Marayu ta Hajiya Maimuna, ranar da cewar ta za ta mayar da hankali wajen nuna so da ƙauna ga marayun. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance:

MANHAJA: Za mu so mu ji taƙaitaccen tarihin baƙuwarmu ta wannan makon?
MAIMUNA: To ni Sunana Maimuna Yusuf. An haifeni a Ƙaramar Hukumar Marte da ke Jihar Borno, kuma babana ɗan jihar ne, mamata kuma ta fito daga Waje ne. na yi karatu tun daga ‘Primary’, ‘secondary’, kafin inzo in shiga Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci “Islamic Learning Centre” daga nan na tsaya na soma harkokin rayuwa. Kuma daga baya na zo na yi aure a Sakkwato, ina da yara.

Me ya ba ki ƙwarin gwiwar tallafa wa marayu?
Na taso a gidanmu, na san babu, kuma na san ciwon a ce mutun na cikin damuwa ta halin rayuwa da sauran su. To sai na ga cewa, ni mace ce, zan iya haihuwar yara, kuma ya zamana cewa, wata rana ma zan iya kasance wa ba na duniyar, to wa zai kulamin da yarana. Ina yawan yin wannan tunanin. Na kan yi tunanin makomar na wa yaran idan na bar duniya. Ita duniya duk lissafin da za ka yi, abu 3 ne, zuwa 4, abinda duk ka samu a nan duniyar, anan za ka tafi ka bar shi. Ba inda za ka je da shi duk mulkin ka, duk kuɗin ka. To wannan tunanin sai ya zauna min a zuciya, kuma bana fatan na mutu a ce na tara dukiya ban taɓa wannan lissafin ba, kawai da zarar na samu abu, burina in bayar da shi a inda na sameshi.

Kamar wane ɓangare ne kika fi tallafa wa?
Ina tallafa wa a dukkanin ɓangarorin karatu, abinci dama sana’o’in dogaro dakai. Kuma fa wannan ba gidauniya ba ce, kawai ina yi ne na ƙashin kai, ba ƙarƙashin wata gidauniya ba. Domin mutane sun sha kiran a maida wannan aikin da na ke gidauniya, ni kuma abinda yasa na ƙi, saboda Allah, don haka ba ya buƙatar suna, saboda shi ‘foundation’, ka san za ka riƙa tattaro kuɗaɗe ne daga wannan, ka haɗa da wannan, domin tafiyar da gidauniyar da ka samar, to a nan zai riƙa dasa ayar tambayar shin kama kai kuɗaɗen da ya baka da sunan za ka bayar da tallafi? Saƙon ya isa inda ake son ya isa? To wannan tunanin sai ya bani damar sauya akalar ayukkana zuwa na ƙashin kai zalla, kuma dama ni kullum a rayuwa ta bana son abinda zai kawo ruɗani tsakanina da mutane.

To, a ina ki ka fi gudanar da ayukkanki?
Duk inda Allah ya kaini ina gudanar da ayukka na, amma na fi ayukka na a jihohin Sakkwato, Kano, Kaduna, Maiduguri da dai sauran su. Kuma galibi na fi tallafa masu ne ta hanyar sayen abubuwa, ina kai masu a IDPs da sauran wuraren buƙatu.

Idan ki ka ga maraya na farin ciki sanadiyyar tallafa ma shi ya kike ji?
Gaskiya na kan ji daɗi sosai, domin galibin lokuta za ka ga idan na je wuraren su za mu yi wasa da dariya, domin mafi akasari sun rasa wannan musamman ma marayu, kuma kullum idan na je na kan ji shauƙi, na ji idan ina da dama zan ci gaba da zuwa har ko yaushe. Kuma ina ganin ma akwai buƙatar gwamnati ta ware masu rana ta musamman a nan Nijeriya, a ce wannan ranar marayu ce, kacokan da aka ware domin amfanin su, kamar yanda ake ware sauran ranaku na girmamawa ga wasu. Kuma ni a karan kaina, na ware ranar 11 ga kowanne watan Maris a matsayin ranar Marayu da zan riƙa zama ina tattauna wa da su, kuma za mu zaɓi jiha ɗaya a ko wacce shekara da za mu riƙa irin wannan bikin ranar, kuma ina son idan har Allah ya sa Atiku ya zama shugaban Nijeriya, wannan ne abu na farko da na ke son ya fara yi, a ce a gwamnatance an ware ranar marayu ta ƙasa, domin a kula da su, lafiyarsu, da nuna masu soyayya, matan a masu aure idan sun isa aure, mazan kuma a koya masu sana’oi da za su riƙa dogaro da kansu.

Maimuna a bakin aiki

Wane abinci ne Hajiya Maimuna ta fi so?
Dariya! Gaskiya na fi son tuwo irin wanda ya kwana haka, wasu lokuta ma nakan yi abinci in aje sai ya kwana kafin inci, inason abincin da ya kwana sosai.

Sutura fa, wane kalar kika fi so?
Na fi son baƙaƙen kaya gaskiya.

Daga ƙarshe, wacce shawara za ki ba wa sauran masu hannu da shuni, na su riqa tallafa wa marayu?
Eh to, dama na sha kira ga shugabanni da su riƙa taimakon marasa shi a rayuwa, domin duk wanda ka taimaka wa a rayuwa, to za ka samu sakamako tun nan duniya, domin taimako wani abu ne da idan kayi shi, tun a nan duniya za ka soma ganin sakamako wajen ubangiji kan abinda kake nema ko kake son samu.
Kuma ya kamata a ce a na tallafa wa matasan ƙasar nan, domin hakan zai rage wasu matsaloli da ake fama da su, a kuma taimaki mata da ƙananan yara da sauran marasa ƙarfi.

Mu na godiya.
Ni ma na gode.