Sanata Binani ta garzaya kotu neman adalci

‘Yar takarar gwamna ta Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa, Sanata Aisha Binani Dahiru, ta garzaya kotu don neman a yi mata adalci a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamna a jihar.

Aisha ta tafi Babbar Kotu a Abuja ne inda ta shigar da ƙarar neman kotu ta dakatar da matakin da Hukumar Zaɓe, INEC, ta ɗauka na soke bayyana ta a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamnan Adamawa bayan zaɓen da ya gudana ranar 18 ga Maris wanda aka kammala ran 15 ga Afrilu.

Kazalika, Sanata Binani na neman kotu ta hana INEC ɗaukar wani mataki na gaba dangane da bayyana wanda ya lashe zaɓen zuwa lokacin da kotu za ta saurari ƙarar da ta shigar.

Ta ce bayan da INEC ta bayyana ta a matsayin wadda ta lashe zaɓe, daga nan jam’iyyar PDP da ɗan takararta Gwamna Ahmadu Fintiri suka tada fitina wanda hakan ya yi sanadin aka lakaɗa wa wani jami’in INEC duka.

Lamarin da ta ce shi ne sanadin da ya sa INEC soke bayyana nasararta da aka yi da farko, wanda a cewarta hukumar ba ta da hurumin yin haka face Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe.

Ƙarar da Binani ta shigar ya shafi INEC ne da kuma Gwamnan Fintiri a matsayin masu kare kansu.

Tawagar lauyoyin Binani ƙarƙashin jagorancin Hussaini Zakariyau, SAN, sun ce kasancewar INEC hukuama ta gwamnati, kotu na da damar bincikar bayanai da ayyukanta, kuma kotu ce kaɗai ke da ikon soke wani aikin jami’in INEC amma ba ita hukumar da kanta ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *