Wanene Jarumi Justus Esiri?

Daga AISHA ASAS

Justus Esiri na ɗaya daga cikin tushe da asalin masana’antar finafinai ta Nollywood, kasancewar sa ɗaya daga cikin waɗanda suka fara yin fim tun kafin ta amshi sunanta na Nollywood a shekarar 1960, inda ya soma da wasan kwaikwayo ta gidan talabijin na NTA, wato Nigerian Television Authority, inda ya fara da wani shiri mai dogon zango da aka yi wa suna da ‘The Village Headmaster’, wanda kusan za a iya cewa ya zama silar shuhurar sa.

Justus Esiri ɗan asalin Jihar Delta ne a Oria-Abraka. An haife shi a ranar 20 ga watan Nuwamban shekarar 1942. Bayan kammala karatun firamare da kuma na sakandire, jarumi Justus Esiri ya tafi Ƙasar Jamus don yin karatunsa na gaba da sakandire a Jami’ar Maximillan University, Munich, German, a shekarar 1964. Sannan ya yi karatu a wasu makarantu kamar Professor Weners Institute of Engineering, West Berlin a shekarar 1967, da kuma Ahrens School of Performing Arts a shekarar 1968.

Sha’awar finafinai ta jarumi Justus ta soma ne a wannan gava, inda ya soma da aiki a matsayin mai fassara a Muryar Nijeriya a Jamus, wato Voice of Nigeria in Germany, daga nan ne ya samu gayyata daga ƙasarsa Nijeriya, inda ta nemi ya zo ya amfani ƙasarsa da ilimin da ya kwankwaɗa na harkar finafinai, tare da uwa uba baiwar da yake da ita ta vangaren, ta hanyar fara fitowa a shirin ‘The Village Headmaster’, kuma ya amsa tayin da aka yi masa, ya dawo gida Nijeriya.

Jarumin ya soma ne daga masana’antar finafinai ta wancan lokacin wadda ake kira da Developing Movie Industry, kuma yana ɗaya daga cikin jaruman da suka samu lambar yabo ta OON, wato Order of the Niger.

Jarumi Justus Esiri ya mutu a sanadiyyar ciwon suga, a ranar 19 ga watan Fabrairu, shekarar 2013, yayin da yake da shekaru 70 da haihuwa. Ya mutu bayan ya bar xa ɗaya a masana’antar, wato shahararren mawaƙi Dakta SID.

Wasu daga cikin finafinai da ya yi sun haɗa da; ‘Wasted Years’, ‘Forever’, ‘The Prize’, ‘Six Demons’, ‘Corridors of Power’, ‘Last Night’, ‘The Tyrant’, ‘The Investigation’, ‘The Ghost’, ‘Assassin Practice’, ‘Doctor Bello’, ‘Twin Sword’, ‘Keep my Will’, ‘Invasion 1897’, da sauransu.