Kotu ta sake aike wa Rarara sammaci

Daga AISHA ASAS

Wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci a Kano ta bada umarnin sake rubuta wa mawaƙi Dauda Adamu Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara wata takardar sammaci sakamakon ƙin halartar zamanta da ya yi.

Kamar yadda jaridar Aminiya ta rawaito, Kotun wacce ke zamanta a unguwar Rijiyar Zaki da ke birnin Kano, ƙarƙashin Mai Shari’a Halhalatul Khuza’i Zakariyya, ta bayar da umarnin yayin zamanta na ranar Talata.

Kamar yadda aka faɗa, ana ƙarar mawaƙin ne kan taurin bashin wasu wayoyin da yake karva, yana rabawa mutane daga wurin wani ɗan kasuwa da ake cewa, Muhammad Ma’aji. Kuɗin wanda ya kai kimanin Naira miliyan goma da dubu ɗari uku.

Barista I. Imam wanda ya kasance lauyan mai ƙara, ya shaida wa kotun cewa, mawaƙin wanda ake ƙara bai mutunta kotu ba, ta hanyar ƙin halartar zaman kotun. Ya kuma roki kotu da ta bayar da damar damƙo mata mawaƙi Rarara sakamakon raina kotu da ya yi. Ya kuma yi birki da tambayar ko saƙon sammacin ya samu isa hannun wanda ake ƙarar, wanda hakan zai tabbatar wa kotu ganganci ne rashin zuwan nasa ko rashin isar saƙon wurin sa.

Da wannan kotun ta buƙaci tabbaci daga bakin jami’inta da ya kai sammacin mai suna Isma’il Zuhudu, kan ko ya samu isar da saƙon hannu da hannu ga wanda aka aike wa da sammacin, wato mawaƙi Dauda Adamu Kahutu Rarara, sai dai ya bayyana cewa, ya liƙa takardar sammacin ne a ƙofar gidan mawaƙin, sakamakon rashin samun damar ganin shi, ido da ido don miƙa takardar hannunsa da nashi.

Tun daga farko dai Mai Shari’a, Halhalatul Khuza’i Zakariyya, ya yi aiken sammaci ga Rarara karon farko kan ƙarar sa da aka kawo wa kotu, inda ake tuhumar sa da lamushe bashin wayoyi na miliyoyin kuɗi, sai dai bai halarci kotun ba kuma bai aiko da wakilinsa ba. Duk da hakan sai kotun ta yi uzuri ga mawaƙin, kasancewar shi ne karo na farko da ya aikata hakan. Sai dai kotun ta sake aike da wani sammacin a karo na biyu, inda ta ba wa ɗan aiken damar liqa takardar a ƙofar gidansa matuqar haɗuwa da shi ya gagara. Sannan kuma aka wallafa a shafukan sada zumunta da kuma kafafen yaɗa labarai, don ganin saƙon ya riske shi a duk inda yake.

Daga ƙarshe kotun ta sanya jiya Alhamis, 13 ga watan Afrilu, 2023, ranar sake zaman sauraren ƙarar.